NAHCON ta fara horar da masu kula da walwalar alhazai yayin shirin Hajjin 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ce ta fara taron kwana biyu domin inganta lamuran kamfanonin masu kula da walwalar alhazai da masu zuwa umara a jihohin Kano da Legas domin ƙarfafa kiyaye harkokin gudanarwa, inganta ayyukansu da gamsar da alhazai gabanin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da Kakakin NAHCON, Shafi’i Sani Mohammed ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, ya ce taron, wanda aka tsara gudanarwa a ranakun 26 da 27 ga Oktoba, 2026, Cibiyar Kula da Lamuran Aikin Hajjin Nijeriya (HIN) ce ta shirya da haɗin-gwiwar Ƙungiyar kula da Walwalar Hajji da Umara ta Ƙasa (AHUON) da Ƙungiyar kula da Jigilar Hajji da Umara ta Ƙasa (HUTON).

Da yake jawabi yayin buɗe taron, Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya ce shirin zai samar da kyakkyawan yanayi na kimtsa masu kula da lamuran hajji da umaran a zamanance ta yadda za su bi sahun masu amfani sakamakon gyare-gyaren da Saudiyya ta samar mai dogon zango zuwa nan da 2030 da kuma tsarin business-to-business (B2B), wanda ya samar da fagen ciyar da lamuran hajji gaba a matakin masu zaman kansu.

Ya bayyana cewa, Nijeriya ta riga ta ƙulla yarjejeniyar bunƙasa harkokin hajjinta da hukumomin Saudiyya, wanda zai fara da kaso 30 ga masu zaman kansu a 2027, domin samar da lokacin ƙarfafa tsarin Nijeriya da shirya kamfanoni ta yadda za su tunkari ƙarin wasu nauye-nauye cikin inganci.

Ambasada Abba Yusuf ya kuma kirayi jami’an hukumomin da su riƙa nuna ƙwarewar aiki, yana cewa ya dace a ke fifita walwalar alhazai sama da la’akari da farashin hidima. Sannan, ya jaddada aniyar hukumar ta tabbatar da sanya ƙwarewa, amfani da fasahar dijital da bunƙasa lamuran gudanarwa domin amfanin alhazai.

A nasa jawabin, Shugaban HIN, Farfesa Muhammad Nasirudeen Maiturare, ya bayyana horarwar aikin a matsayin abu mai muhimmanci ga gudanarwar lamuran hajji a zamanance, yana mai bayar da misalai da ƙwarewa a jagorancin haɗaka, gudanar da muhimman ƙalubale, tsara ayyuka da tsare-tsaren hidimar matakin ƙasa-da-ƙasa. A kwanan nan ne Saudiyya ta ɗauki matakin ƙara wa Nijeriya guraben alhazai daga karɓar mutum 50,000 zuwa 60,000, bayan ta amince wa buƙatar Nijeriyar da aka gabatar mata a lokuta mabambanta.

By Babaji

Leave a Reply