
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni daga Arewa maso Yammacin Nijeriya sun ce, a daren nan ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki tare da halaka fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Yahaya Masussuka tare da wani baƙonsa mai suna Malam Adamu a garin Dustin-Ma da ke Jihar Katsina.
Majiyoyi sun ce, maharan sun je yankin ne akan wani babur, inda suka buɗe wa malamin wuta a lokacin da yake shiga gidansa bayan ganawa da baƙon a ranar Litinin.
Wannan hari ya yi sanadiyyar mutuwar Sheikh Masussuka da Malam Adamu, a cewar majiyoyi masu masaniya kan al’amarin.
An yi wannan kisa ne yayin da malamin ke shirin halartar taron zaman lafiya da haɗin kai da aka tsara gudanarwa a ranar 31 ga Oktoba, 2026. Saidai babu wani cikakken bayani kan harin, musamman kan abin da ya shafi maharan da ainihin manufarsu.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, babu wani ƙarin bayani kan aukuwar lamarin.
Sauran bayanai za su biyo baya…
