DSS ta maka ɗan Kaduna a kotu kan wasiƙar bogi ta Tinubu zuwa ga Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta shigar da ƙarar tuhume-tuhume guda uku na laifukan da suka shafi yanar gizo akan wani ɗan Kaduna bisa zargin sa da yaɗa wata wasiƙar bogi da aka ce wai Shugaba Bola Tinubu ne ya rubuta ta zuwa ga Shugaba Donald Trump na Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama wanda ake zargin mai suna Mubarak Abdullahi da aka sani da Sardaunan Samari ne a ranar 28 ga Satumba, 2026 bayan an zarge shi da yaɗa takardar a shafinsa na Facebook tare da taken, “Atiku is Coming.”

Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya bayar da wannan labari a shafinsa na X a daren wayewar Talata, 27 ga Oktoba, 2026 inda ya ce an gurfanar da Abdullahi Abubakar a gaban alƙalin Babbar Kotun Shari’a mai Lamba ta 10 da ke Kabala Doki a Jihar Kaduna. A wallafar, Onanuga ya bayyana wanda ake zargin a matsayin fitaccen mai goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar kuma ya ce yana fuskantar shari’a ne kan yaɗa wata wasiƙa da aka ce Tinubu ne ya rubuta ta ga Shugaban Amurka.

Ya ƙara da cewa, Abdullahi ya amsa wa masu bincike cewa ya yaɗa takardar amma yana bayar da haƙuri akan haka, saidai haƙurin nasa bai wadatar ba kan matakin shari’ar da aka ɗauka akansa. A cewar Onanuga, DSS ta gurfanar da Abdullahi Abubakar gaban kotun Chief Magistrate Court No. 10, Kabala Doki, Kaduna, wadda ta umarci a tsare shi a gidan gyaran hali da ke Kaduna.

Ya bayyana cewa, hukumar ta kuma shigar da ƙarar tuhume-tuhume guda uku masu alaƙa da laifukan yanar gizo da ɓatanci akan wanda ake zargin a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, yana mai cewa DSS za ta cigaba da amfani da ikon da doka ta ba ta na gano masu yaɗa ababen da ke ruɗar da jama’a a shafukan sadarwa.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, Atiku ko mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu ba su fitar da wani saƙo kan al’amarin ba.

By Babaji

Leave a Reply