Shugaban ƙaramar hukumar Bursari ya rantsar da kansiloli, ya raba mashin roba-roba

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari ta Jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar Guba, ya rantsar da kansiloli, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar da sakataren ƙaramar hukumar, a wani mataki na ƙarfafa tafiyar da harkokin mulkin ƙaramar hukumar.

Bayan rantsar da jami’an, Hon. Lawan Bukar Guba ya kuma gudanar da shirin tallafa wa al’umma, inda aka raba mashin roba-roba ga waɗanda suka ci gajiyar shirin domin taimaka musu wajen samun sabbin hanyoyin dogaro da kai, inganta sana’o’insu da bunƙasa rayuwarsu. Shirin na daga cikin ƙoƙarin ƙaramar hukumar na ƙarfafa tattalin arzikin al’umma da samar da damammakin inganta rayuwa.

A nasa ɓangaren, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar ƙaramar Hukumar Bursari, Hon. Zanna Baba Gana, ya taya shugaban ƙaramar hukumar da dukkan jami’an da aka rantsar murna.

Ya yi musu fatan samun nasarar sauke nauyin da aka ɗora musu, tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon gudanar da ayyukansu cikin adalci, gaskiya da kishin al’umma.

Ana fatan shirin tallafin zai taimaka wajen ƙarfafa dogaro da kai, samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga da inganta rayuwar waɗanda suka amfana da shi a ƙaramar Hukumar Bursari.

By ukarofi

Leave a Reply