Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yau ne aka gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a fadar Sarkin Katsina bayan da aka kammala sallar Juma’ah.
Saboda yawan mutane da suka halarci jana’izar dole tasa gawar tasa yana cikin motar ɗaukar marasa lafiya aka yi masa jana’iza.
Tunda safiyar yau juma’a akai ta ganin motoci ɗauke da mabiya, malamai,yan uwa da abokan arziki daga ciki da wajan ƙasar nan suna turuwa zuwa fadar sarki inda aka gudanar da sallar jana’izar marigayi Sheikh Masussuka.
Imam Rasheed Masussuka ɗalibin sa,surikin sa wanda ana yi masa kallon wanda yana iya maye gurbin Sheikh Masussuka ya jagoranci kai gawar zuwa maƙabarta Abbatuwa a garin Katsina.
An dai rufe Masussuka kusa da abokan sa Adam Abubakar Nasarawa ɗan ƙaramar hukumar Doma.
Litinin da ta wuce wasu da ba a san ko su waye ba suka harbi Sheikh Yahaya Masussuka da abokin sa Adam Abubakar a ƙofar gidan Masussuka inda nan take suka rasu.
Tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bada umurnin gudanar da cikakken bincike da gano waɗanda suka aikata wannan ta’adanci.
