
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla ɗalibai guda 12 na makarantar Madarasatul Nurul Islam da ke yankin Maikuheri na Ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su. Rahotanni sun ce, al’amarin ya auku ne a ranar Asabar a lokacin da yaran suke nome masara a gonar malaminsu da ke wajen garin.
Wani mazauni Mohammed Adamu, ya shaida wa wakilinmu cewa, al’amarin ya faru ne a lokacin da yaran suke kan hanyar komawa gidajensu, inda ‘yan bindiga suka farmake su tare da yin awon-gaba da su. A yayin haka, an harbi wani ɗan acaɓa mai suna Tasi’u a lokacin da ya yi yunƙurin tserewa, wanda a yanzu yake karɓar magani Asibitin IBB Specialist Hospital da ke Minna, babban birnin jihar.
Saidai, wata majiya mai kusanci da makarantar ta shaida wa ‘yan jarida cewa mutane 13 ne aka sace, ciki har da ɗan uwan mai makarantar, Malam Mainasara. A cewarta, waɗanda aka sace yara ne masu shekaru tsakanin 9 da 14, da aka yi awon-gaba da su a lokacin da suka yasar da zango a wata rijiyar burtsatse domin wanke jikkunansu kuma su sha ruwa bayan sun kammala aikin gonar.
Ta ƙara da cewa, suna aiki a gonar ne tare da malamin nasu a lokacin da ya samu labarin cewa ‘yan bindiga sun tunkaro yankin nasu. Akan haka ne ya umarci da su hanzarta tafiya gidajensu, inda shi ma ya bar babur ɗinsa a gonar tare da yunƙurin nema mafaka.
Kazalika, majiyar ta ce an kuma sace wasu mata a wata gona da ke yankin. A lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alƙawarin cewa za su tantance labarin tare da fitar da bayani a kai. Amma ya ce an ceto mutum shida, saidai bai fayyace ko hakan na da alaƙa da batun sace ɗaliban ba.
Ya ce, a ranar 29 ga Oktoba, 2026 da misalin ƙarfe 12:30 na rana ne jami’an tsaro suka ƙaddamar da aikin ceton a yankin Pandogari da ke Ƙaramar Hukumar Rafi, inda suka ceto mutane shida da aka sace a ranar 28 ga Oktoba, 2026 da ƙarfe 12 na rana a gonakinsu da ke ƙauyen Mahangi ta yankin Pandogari, sannan aka garzaya da su zuwa yankin Hanawanka. Bayan ceto su kuma an kai su babban ofoshin jami’an tsaro na Kagara domin duba lafiyarsu kafin a damƙa su ga iyalansu.
