Za a kammala sanya idanu kan waɗanda suka yi mu’amala da mai cutar Ebola 62 Nuwamba 13 – NCDC

Spread the love

Daga Usman Karofi

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa mutane 62 da aka gano sun yi mu’amala da mutumin da aka tabbatar yana ɗauke da cutar Ebola da aka shigo da ita Najeriya, ana sa ran za su kammala wa’adin sa ido a kansu zuwa ranar 13 ga Nuwamba, 2026. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta kan halin da ake ciki game da cutar Ebola, inda ta ce lokutan kammala sa ido kan mutanen sun fara ne daga 31 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba, 2026. Sai dai hukumar ta ce aikin gano mutanen da suka yi mu’amala da mai cutar da kuma sa ido a kansu na ci gaba da gudana.

NCDC ta kuma bayyana cewa tana ƙara ƙarfafa ayyukan sa ido ta hanyar horar da ƙarin jami’an bin diddigin waɗanda suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar. Haka kuma, hukumar na shirin tantance wasu ƙarin mutane domin yiwuwar kai su cibiyar killacewa, tare da ci gaba da sa ido kan waɗanda tuni suke ƙarƙashin killacewa. Rahoton ya kuma nuna cewa an gudanar da gwaje-gwajen Ebola guda 18 tun bayan tabbatar da bullar cutar, inda guda daya ya nuna sakamakon kamuwa da cutar, yayin da guda 17 suka nuna babu cutar. Daga cikin gwaje-gwajen da suka nuna babu cutar, guda 15 na mutanen da suka yi mu’amala da majinyacin ne, yayin da guda biyu kuma na waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar ne.

Dangane da matakan daƙile yaɗuwar cutar, hukumar ta ce an kammala shirin ayyukan gaggawa tare da kunna tsarin kula da aukuwar annoba na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate. Haka kuma, an kammala tantance shirye-shiryen asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja domin ya zama cibiyar killacewa da kula da masu ɗauke da cutar. NCDC ta ƙara da cewa za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomi da abokan hulɗa, faɗada ƙarfin ɗakunan gwaje-gwaje, da kuma inganta shirye-shiryen jihohin da ake ganin suna cikin haɗarin fuskantar ɓullar cutar.

By ukarofi

Leave a Reply