Shugaban ƙaramar hukumar Bade ya rantsar da mataimakinsa da kansilolinsa 10

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar hukumar Bade da ke Jihar Yobe, Hon. Musa Kalan Dagona, ya rantsar da mataimakinsa da kansilolinsa 10 a gidan Gwamnati da ke Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar.

Bayan rantsar da su, Hon. Musa Kalan Dagona ya bayyana cewa ba zai lamunci rashin ɗa’a ba, inda ya yi kira ga ma’aikatan ƙaramar hukumar da su riƙa zuwa wuraren aikinsu a kan lokaci.

A nasa jawabin, ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Yobe mai wakiltar Bade ta Yamma, Hon. Umar Sanda Karabade, ya yi magana kan buƙatar samar da ingantaccen ruwan sha ga al’ummar mazabun ƙaramar hukumar Bade, inda ya buƙaci shugaban ƙaramar hukumar da ya mai da hankali kan wannan muhimmin al’amari.

Shi ma ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Yobe mai wakiltar Bade ta Gabas, Hon. Yahaya Attajiri Yadau Alwashin, ya yi magana kan babban zaɓe mai zuwa, inda ya bayyana cewa ɗan takarar gwamnan Jihar Yobe na jam’iyyar APC, Hon. Baba Mallam Wali, zai samu nasara a zaɓen, insha Allah.

Daga wakilin jaridar Blueprint, Alhaji Hassan Bulama, a Gashua, ƙaramar Hukumar Bade, Jihar Yobe.

By ukarofi

Leave a Reply