Taron Shettima: Gwamna Sule ya nemi DSS su binciki Al-Makura

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Nasarawa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna A.A Sule ta buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gudanar da bincike kan abin da ta bayyana a matsayin “munanan ayyuka” da wasu matasa da suka fusata suka aikata a lokacin ziyarar Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a jihar ranar Laraba.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da ta fitar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Shuaibu Labaran, ya ce Shettima ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Lafia, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa, a wani ɓangare na gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen 2027.

Gwamnatin ta ce abin takaici ne yadda wannan ziyarar girmamawa ga masarautar, wadda Shettima ya ɗauka a matsayin nuna girmamawa ga al’ada, ta samu tangarɗa sakamakon wasu munanan ayyuka da wasu matasa da suka fusata suka aikata.

Labaran ya ce ana zargin matasan da alaƙa da wasu manyan mutane, ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, da tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Muhammad Adamu.

Ya yi zargin cewa an aikata waɗannan abubuwa ne da nufin ɓata sunan gwamnatin jihar da kuma al’ummar Nasarawa.

Sanarwar ta ce: “Wannan ganganci da aka aikata da gangan domin nuna rashin biyayya ga hukumomin da doka ta kafa, da kuma nuna rashin girmamawa ga babban ofishin Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya, abin Allah-wadai ne kuma ba za a amince da shi ba.”

Saboda haka, gwamnatin ta umarci DSS da ta gudanar da bincike kan lamarin, gano waɗanda ke da hannu a ciki tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Saboda haka, an umarci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya da ta fara cikakken bincike nan take domin gano musabbabin faruwar lamarin, waɗanda suka aikata shi da kuma waɗanda suka ɗauki nauyin wannan abin Allah-wadai, tare da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.”

Gwamnatin ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu bin doka da oda yayin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai ɗanjuma Joseph, wanda ke da alaƙa da Al-Makura, ya yi watsi da zargin a wata sanarwa ta daban, inda ya bayyana shi a matsayin zargi marar tushe, mai cike da ƙeta da kuma yunƙurin karkatar da hankalin jama’a daga yadda Gwamna Abdullahi Sule ya gudanar da al’amura da kuma rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar APC.

Joseph ya yi zargin cewa Gwamnan ya yi amfani da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa wajen tallata muradunsa na siyasa da kuma burin Sanata Ahmed Aliyu Wadada na zama gwamnan jihar.

Ya ce: “An shirya gangamin ne domin tattara goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Amma maimakon haka, Gwamna Sule ya mayar da shi wata dama ta tallata muradunsa na siyasa, inda ya riƙa maimaita taken ‘Wadada for Goɓernor!’ tare da tallata burin Sanata Ahmed Aliyu Wadada na zama gwamna.”

Ya ce an shirya gangamin APC ne domin neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu, don haka bai kamata a yi amfani da shi wajen tallata wanda gwamnan yake so ya gaje shi ba.

Joseph ya ƙara da cewa: “Gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ba dandali ne na musamman na Gwamna ba. An shirya shi ne domin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu, ba domin gudanar da bikin naɗa wanda yake so ya gaje shi tun da wuri ba.”

Joseph ya ce lamarin ya samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafe da suka daɗe suna addabar jam’iyyar APC a Nasarawa, tun bayan zaɓen fidda gwani na gwamna da aka gudanar a watan Mayu, wanda ya ce mambobin jam’iyyar da dama ke ganin ba a yi adalci ba.

Ya ce: “Mutane da dama na ganin an mayar da su saniyar ware, an tauye musu haƙƙoƙinsu, kuma an zalunce su a tsarin da ya samar da Sanata Wadada a matsayin ɗan takara.”

Ya kuma zargi Gwamnan da yin watsi da ƙorafe-ƙorafen da ke cikin jam’iyyar, sannan yana ƙoƙarin ɗora laifin kan tsohon gwamna wanda ya bayyana a matsayin mutumin da ke tsayawa kan adalci, daidaito da dimokuraɗiyyar cikin gida ta jam’iyya.

Joseph ya ce: “Rashin gaskiya ne Gwamnan ya yi kamar bai san da waɗannan ƙorafe-ƙorafe ba, sannan ya zargi tsohon Gwamna mai daraja wanda a ko da yaushe yake tsayawa kan adalci, daidaito da dimokuraɗiyyar cikin gida ta jam’iyya.

“Mun yi watsi da yunƙurin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Labaran Shuaibu Magaji, SAN, na danganta sunan Sanata Al-Makura da wannan lamari ba tare da wata sahihiyar hujja da za a iya tantancewa ba.”

Joseph ya dage cewa idan gwamnati tana da hujja kan duk wani mutum, ya kamata ta miƙa ta ga ’yan sanda domin su gudanar da aikinsu bisa doka, maimakon amfani da sanarwar manema labarai wajen ɓata sunan abokan hamayyar siyasa.

Ya kuma ce tuni ’yan sanda suka kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a lamarin, inda ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike cikin ƙwarewa ba tare da katsalandan na siyasa ko gallazawa ba.

Wannan zarge-zarge na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rashin jituwa ta siyasa tsakanin Al-Makura da Gwamna Sule. A watan Mayu, Gwamnan ya zargi tsohon gwamnan da ƙoƙarin zaɓar wanda zai gaje shi.

Wa’adin mulkin Gwamna Sule na shekaru takwas, wanda kundin tsarin mulki ya ba shi damar yi, zai ƙare a shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply