
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato ya sanar da ƙara alawus ɗin wata-wata da ake bai wa ‘yan hidimar ƙasa (NYSC) daga Naira 10,000 zuwa N20,000 a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin buɗe taron horar da ‘yan Rukunin ‘C’ ɗiba na biyu a sansanin wucin-gadi da ke Sashen Kwalejin Nazarin Gudanarwar da Kasuwanci na Polytechnic ta Umar Ali Shinkafi ta Farfaru a Sakkwato.
Baya ga haka, ya kuma amince da bai wa kowane ɗaya daga cikin su 1,523 kyautar N30,000 da suka halarci wajen karɓar horon.
Da yake jawabi kan bashin da gwamnatocin jihohi suke riƙewa na kuɗaɗen alawus, gwamnan ya ce an kafa kwamiti domin gudanar da aikin nazari da ɗaukar mataki a kai bayan ƙorafi daga kodinetan NYSC na jihar. Ya umarci a fara biyan sabon alawus ɗin a nan take. Haka kuma, ya tallafa wa shirin NYSC da sabuwar mota ƙirar Hilux ga kodinetan domin gudanar da harkokin hukumar.
Kazalika, ya umarci a gaggauta gyara kayayyakin samar da wuta da ruwa a sansanin domin inganta walwalar ‘yan hidima. Gwamnan, ya kuma amince da yanka musu shanu biyar a kullum domin faɗaɗa walwalar abinci.
