Daga AISHA ASAS
Bayan shafe sama da shekaru talatin tana gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Yammacin Sahara, Majalisar ɗinkin Duniya ta fara kawo ƙarshen aikin rundunar MINURSO, sakamakon rashin samun matsaya tsakanin manyan ƙasashen duniya kan makomar yankin.
A ranar Lahadi, 1 ga Nuwamba, 2026, Majalisar ta tabbatar da cewa wa’adin aikin rundunar ya ƙare bayan ƙasashe mambobin Kwamitin Tsaro sun kasa cimma matsaya kan ƙudurin tsawaita aikinta. Rashin samun matsayar ya biyo bayan takaddama tsakanin Amurka da Rasha. Amurka ta gabatar da wani ƙuduri da ke goyon bayan matsayin Morocco kan yankin, sai dai Rasha ta yi amfani da ƙarfinta na veto wajen dakatar da shi. Haka kuma, wani ƙudurin da Rasha ta gabatar domin tsawaita aikin rundunar bai samu ƙuri’un da ake buƙata ba.
An kafa rundunar MINURSO ne a shekarar 1991, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, domin sa ido kan zaman lafiya da taimakawa wajen gudanar da zaɓen raba gardama da zai bai wa al’ummar yankin damar yanke makomarsu. Sai dai wannan zaɓe bai taɓa gudana ba, saboda rashin jituwa tsakanin ɓangarorin da ke takaddama kan waɗanda ya kamata su cancanci kada ƙuri’a. ƙarshen aikin rundunar ya haifar da martani daban-daban. Yayin da Morocco ta nuna maraba da matakin, ƙungiyar Polisario da Algeria sun bayyana rashin jin daɗinsu.
Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, António Guterres, ya jaddada cewa ƙarshen aikin MINURSO ba yana nufin an ƙwace wa al’ummar Yammacin Sahara haƙƙinsu na zaɓar makomarsu ba. Ya kuma yi gargaɗin cewa akwai buƙatar dukkan ɓangarorin su guji matakan da za su iya ƙara dagula tsaro a yankin.
Haka kuma, Majalisar ta fara shirye-shiryen janye ma’aikata da kayayyakin rundunar, yayin da za a ci gaba da ƙoƙarin samun mafita ta hanyar diflomasiyya.
