Abdul El-Sayed ya zama Musulmi na farko a Majalisar Dattawan Amurka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dan takarar jam’iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya lashe zaɓe a Jihar Michigan ta Amurka, inda zai kafa tarihi a matsayin Musulmi na farko da ya samu kujerar Majalisar Dattawan ƙasar, bayan fafatawar da ta ƙunshi munanan hare-haren siyasa da saɓani tsakanin ’yan jam’iyya.

El-Sayed ya doke ɗan takarar jam’iyyar Republican, Mike Rogers, duk da ya fuskanci hare-hare da suka haɗa da ƙoƙarin danganta shi da ta’addanci ba tare da wata hujja ba, da kuma rikicin da ya yi da wata ’yar jam’iyyarsa ta Democrat. Rogers, wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya mara wa baya, ya riƙa bayyana El-Sayed a matsayin ɗan gurguzu, tare da sukar matsayinsa kan Isra’ila da kuma addininsa na Musulunci.

Bayan shafe tsawon sa’o’i ana jiran sakamakon zaɓe, tare da kallon yadda ’yan Democrat ke samun nasarori a sassan ƙasar, magoya bayan El-Sayed sun yi murna matuƙa lokacin da ya fito kan dandamali domin bayyana nasararsa. Tsohon jami’in kula da lafiyar jama’a ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa ne bisa manufofin masu ra’ayin hagu, waɗanda suka haɗa da samar da tsarin kula da lafiyar jama’a ga kowa da kowa, da kuma sanya harajin dukiya ga hamshaƙan attajirai.

Nasarar tasa ta zo ne kwanaki kaɗan bayan abokiyar hamayyarsa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Democrat, Haley Stevens, ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar Republican, Mike Rogers, kwanaki kaɗan kafin zaɓen.

Magoya bayan El-Sayed sun yi ta shewa da sowa lokacin da ya hau dandamali, suna rera sunansa cikin farin ciki. Mutane da dama sun ɗaga wayoyinsu domin ɗaukar wannan lokaci mai cike da tarihi, na zaɓen wani Musulmi zuwa Majalisar Dattawan Amurka. Wasu daga cikin mutanen da ke wajen sun rungumi juna cikin tsananin farin ciki da motsin rai. Sun riwa maimaita taken yaƙin neman zaɓensa kamar yadda ake yi a wurin shagalin kiɗa, inda suke cewa: “A cire kuɗi daga harkokin siyasa, a mayar da su aljihun jama’a, sannan a samar da tsarin kula da lafiyar jama’a ga kowa.”

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, El-Sayed, wanda ɗa ne ga wasu ’yan gudun hijira daga Masar da suka yi ƙaura zuwa Amurka, ya bayyana ayyukan Isra’ila a Gaza a matsayin kisan kare dangi, tare da kira da a dakatar da tallafin da Amurka ke bai wa Isra’ila.

Wannan batu yana da matuƙar muhimmanci a Michigan, domin jihar ce ke da al’ummar Larabawa-Amurkawa ta biyu mafi yawa a Amurka. Batun ya kuma ƙara tsananta saɓani tsakanin El-Sayed da Stevens, wadda ke da cikakken goyon bayan Isra’ila. Yaƙin neman zaɓen fidda gwanin Stevens ya samu tallafin kuɗi na miliyoyin daloli daga ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Amurka da Isra’ila (AIPAC).

An ɗauki wannan fafatawa a matsayin gwajin irin tasirin da masu ra’ayin hagu na jam’iyyar Democrat ke da shi a wata muhimmiyar jiha da ake fafatawa sosai a zaɓe, musamman bayan jerin nasarorin da ’yan takarar gurguzu masu ra’ayin dimokuraɗiyya suka samu a wasu yankunan da jam’iyyar ke da rinjaye.

Da sanyin safiyar Laraba, El-Sayed ya gode wa magoya bayansa bisa yadda suka ba shi dama duk da kasancewarsa ɗan takarar da mutane da dama ba su yi tsammanin zai iya yin nasara ba. Ya kuma yi kakkausar suka ga abokan hamayyarsa. Ya ce, “Sun yi amfani da dukkan ƙarfinsu wajen gudanar da ɗaya daga cikin mafi munin yaƙin neman zaɓe da muka gani cikin dogon lokaci.”

Ya zargi abokan hamayyarsa da kai masa hari saboda sunansa da addininsa. “Sun so Amurka wadda ba za ta wadatar da wasu daga cikinmu ba. Amma mun san cewa Amurka ƙasa ce da za ta iya ɗaukar mu duka,” inji shi.

Wannan nasara ta kasance wani babban tarihi ga Musulman Amurka, waɗanda suka riƙa kallon yadda ake kai wa El-Sayed hare-hare bisa ƙiyayya ga Musulunci, har ma da kalaman da Shugaban Amurka da kansa ya yi. Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ƙiyayya da tsangwama ga Musulmi ke ƙaruwa a sassan ƙasar. Roula Allouch, wata Ba’amurkiyar asalin Larabawa kuma Musulma, ta shaida wa BBC cewa nasarar yaƙin neman zaɓen ta sa fatarta ta tashi saboda farin ciki. Ta ce, “Ina alfahari da Abdul, da irin yaƙin neman zaɓen da ya gudanar, da kuma iyalinsa bisa juriyar da suka nuna duk da ƙiyayya da kalaman nuna wariya ga Musulunci da aka riƙa jifansa da su a tsawon wannan yaƙin neman zaɓe.”

Wata Musulma da ke cikin taron ma ta nuna irin farin cikin da ta ji, inda ta shaida wa BBC cewa nasarar El-Sayed tana da matuƙar muhimmanci a gare ta. Ta ce, “Yana sa mu alfahari sosai, kuma hakan yana sa mu ji cewa za mu iya ɗaga kai da ƙwarin gwiwa, domin mun san akwai wanda zai tsaya mana a Washington, yana fafutukar kare muradunmu.”

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, El-Sayed ya nuna cewa ba zai yi shiru ba idan aka kai masa hari daga magoya bayan ƙungiyar siyasar MAGA ta Trump.

A jawabinsa na murnar nasara, ya yi amfani da kalmar Larabci “Alhamdulillah”, sannan ya yi wa ’yan Republican habaici, yana cewa ga masu tsattsauran ra’ayin dama, wannan na nufin “godiya ta tabbata ga Allah.”

El-Sayed mai shekaru 42 ya wakilci sabon ƙarni na Larabawa-Amurkawa da Musulman da aka haifa a Amurka, bayan iyayensu sun yi ƙaura zuwa ƙasar, kuma suka taso a lokacin da Amurka ke fuskantar sauye-sauyen da suka biyo bayan hare-haren 11 ga Satumba, 2001.

Wata Musulma ‘yar asalin Kudancin Asiya, wadda ta je bikin nasarar tare da iyalinta daga Chicago, ta ce wannan lokaci tarihi ne ga duk mutanen da aka taɓa nuna wa cewa ba su da gurbi ko matsayi a Amurka ko kuma a harkokin siyasar ƙasar. Ta ce, “Idan mutum mai suna Abdul ya iya samun wannan matsayi, hakan yana nuna wa sabon ƙarni cewa su ma za su iya cimma irin wannan nasara.”

Kujerar Majalisar Dattawan Amurka ta Michigan, wadda Sanata Gary Peters na jam’iyyar Democrat mai shirin yin ritaya ya riƙe a baya, na daga cikin kujerun da manazarta suka yi hasashen za a fafata sosai a kansu a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na ranar Talata. Nasarar El-Sayed ta ƙara tabbatar da rinjayen jam’iyyar Democrat a Majalisar Dattawan Amurka, bayan da jam’iyyar ta samu jerin nasarori, ciki har da wasu yankunan da jam’iyyar Republican ta daɗe tana da ƙarfi.

El-Sayed ya fuskanci ƙalubalen kashe maƙudan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe daga ƙungiyoyin da ba sa ƙarƙashin jam’iyyarsa, waɗanda suka fi karkata ga tallafa wa Rogers da kuma abokiyar hamayyarsa a zaɓen fidda gwanin Democrat, Haley Stevens. Duk da haka, bai sauya matsayinsa kan manufofinsa ba, kuma bai nuna nadama kan ra’ayoyinsa ba.

By ukarofi

Leave a Reply