APC a Kebbi ta zargi ADC da tada fitina a Argungu

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR, Birnin Kebbi.

Jam’iyyar APC ta Kebbi ta fusata matuƙa dangane da yadda ‘yan bangar jam’iyyar ADC da ke ɗauke da muggan makamai da aka yo haya, suka farma magoya bayan APC a Argungu a lokacin yaƙin neman zaɓen ɗan takaran shugaban ƙasa na ADC da ya zo Kebbi.

Mai bai wa gwamnan Jihar Kebbi Shawara na musamman akan siyasa da lantarki, Kabir Sani Giant, ya gaya ma ‘yan jarida a Birnin Kebbi cewar, jam’iyyar adawa ta ADC ta shigo da ‘yan bangan siyasa guda 500 daga Sokoto zuwa Kebbi ɗauke da adduna da wuƙaƙe da takubba da barandami da sauran nau’in makami.

Ya ce a sa’ilinda jerin gwanon Atiku Abubakar na yaƙin neman zaɓe suna dab da shiga Argungu, ‘yan bangan siyasa na ADC da ke ɗauke da makamai suka diran ma bilbod-bilbod da motoci na APC, suka rusa su, suka bubbugesu, suka lalatasu, sannan kuma da suka shiga cikin garin Argungu, suka farfasa ofis na APC suka cinna mashi wuta, suka ƙoneshi.

Kabir Giant ya ce ‘yan jam’iyyar APC sun ɗauki matakin kariya a lokacin harin, domin ceton rayukansu da dukiyoyinsu.

Ya ce wannan aika-aika na ADC abin kushewa ne da kuma tir da shi, yana mai cewar duk jam’iyyar da tayi amanna zata yi nasara a zaɓe ba zata kai wa al’umma hare-haren ta’addanci na siyasa ba.

Kabir Giant ya ce ADC ta rigaya ta ga zahiri, cewar babu nasara a tafiyarta, wadda ko kujerar kansila ba za ta iya ci ba idan anyi zaɓe.

Mai bai wa gwamnan shawara ya yi bayanin cewar ɗan takaran gwamnan Kebbi na ADC Abubakar Malami, ya zaƙu ya koma mulki domin ya samu kariya daga hukumcin da ke jiransa a kotu, dangane da abubuwan da ya tabka akan mulki a matsayinsa na ministan shari’a da ya fi kowa iko a lokacin gwamnatin marigyayi tsohon shugaban ƙasa, Buhari.

Ya ce wannan ba shine karo na farko ba da Malami ya kawo hatsaniya a Kebbi, amma yaƙini yake cewar jama’ar Kebbi sun san kowanene Malami, sun juya mashi baya, kuma ba zai taɓa zama gwamnan jihar ba.

Kabir Giant ya ce APC ta tausasa zukatan magoya bayanta su wanzar da zaman lafiya da sadaukar da kai, domin babu wata barazana da jam’iyyar ADC za ta yi ma APC mai mulki.

By ukarofi

Leave a Reply