Rundunar sojan Nijeriya ta ƙwato shafinta na X bayan watanni

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da dawo da sahihin shafinta na X, @HQNigerianArmy, inda ta tabbatar da cewa a yanzu shafin ya koma ƙarƙashin gudanarwarta bayan tsawon lokaci na ƙoƙarin ƙwato shi.

Rundunar ta sanar da wannan ci-gaba ne a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026 a wani taƙaitaccen saƙo da ta wallafa a X ɗin nata, inda ta yi wa al’umma godiya bisa haƙuri da fahimtar su. “Shafin ya dawo kuma zai cigaba da aiki a ƙarƙashin gudanarwar Rundunar Sojin Nijeriyar. Mu na godiya ga haƙuri da fahimtarku.”

Wannan na zuwa ne bayan wani yunƙurin kutse da aka yi wa shafin a ranar 29 ga Agusta, 2026 da aka gano, wanda Daraktan Hulɗa da Jama’ar sojin, Kanal Appolonia Anele ya tabbatar kuma ya ce rundunar tana aiki a kai.

A lokacin da aka gano yunƙurin kutsen, wanda ya faru da misalin ƙarfe biyar ɗin 29 ga Agusta, jami’an gudanarwarta sun ɗauki matakan gyara da ankarar da al’umma kan halin da kuma ƙoƙarin bayar da kariya ga sake aukuwar irin haka a nan gaba.

Ta kuma umarci ‘yan Nijeriya da su riƙa dogara da sahihan shafukanta na sada zumunta wajen neman sahihan bayanai. Shafukan sun haɗa da na Facebook da Instagram a ƙarƙashin sojin Nijeriya na @hqnigerianarmy da @nigerianarmyinfo, na X @nigerianarmyinfo, da kuma tashoshin YouTube.

By Babaji

Leave a Reply