Ƙoƙarin da Gwamnatin Tinubu ta yi wajen aikin hanyar Kano zuwa Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD

Idan aka yi magana kan hanyar Kano zuwa Katsina, gaskiya ɗaya ce da kowa ya sani Tinubu bai fara wannan hanya ba amma inda ba tare da gudummawar gwamnatinsa ba, hanyar da ta shafe shekaru 10 tana tafiyar hawainiya, da ta mutu gaba ɗaya.

Hanyar Kano zuwa Katsina mai tsawon 152km, an raba ta gida biyu:

Sashi na ɗaya mai tsawon 74.1km An ba da shi a 2013 a zamanin Jonathan akan N14 Biliyan.
Sashi na biyu mai tsawon 79.5km An ba da shi a 2019 a zamanin Buhari akan N29 Biliyan.

Lokacin da Tinubu ya hau mulki a Mayu 2023, Section II ya kamata a kammala shi tun 12 ga Yuli 2023, amma bai kammala ba. Sashi na biyu kuma ya yi nisa amma bai kammala ba.

Ma’aikatar Ayyuka ta ce dalilin jinkiri shi ne: rashin kuɗi, hauhawar farashi, da matsalar diyya.

Tinubu da ya watsar da aikin kamar yadda wasu gwamnatoci ke yi wa ayyukan magabata. Amma ya zaɓi ya ci gaba da aikin.

Babbar matsalar hanyar tun farko ita ce rashin kuɗi. Gwamnatin Tinubu ta magance wannan matsala ta hanyar sanya kuɗi kai tsaye a kasafin kuɗi.

A kasafin 2024 da 2025 sashi na ɗaya na aikin hanyar an sanya N6 Biliyan a 2024, N34 Biliyan a 2025.
Sashi na biyu, an sanya N80 Biliyan a cikin shekaru biyu

Jimilla, Gwamnatin Tinubu ta sanya N120 Biliyan a cikin shekaru biyu kacal don wannan hanya ɗaya.

Bugu da ƙari, a cikin kasafin 2025, ma’aikatar ayyuka ta Katsina ta bayyana cewa an tanadi N75 Biliyan a matsayin Budget Provision don aikin sashin na biyu kaɗai.

Wannan shi ne kuɗi mafi girma da aka taɓa sanyawa wannan hanya a tarihi.

A shekarar 2025, majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ƙarƙashin Shugaba Tinubu a zaman da ta yi ta yanke hukunci mafi girma kan wannan hanya
Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana wa manema labarai bayan taron “Sashi na ɗaya, wanda aka ba a 2013 akan N14 Biliyan, aka sake duba zuwa N24 Biliyan, yanzu ya koma N68 Biliyan. Sashi na biyu, wanda aka ba a 2019 akan N29 Biliyan, aka sake duba zuwa N46 Biliyan, yanzu ya koma N66.115 Biliyan.”

Jimillar kuɗin hanyar yanzu ya kai N134 Biliyan ministan ya ce.

Wannan sake dubawa ya zama wajibi saboda farashin siminti, ƙarfe da man fetur ya ninka sau uku zuwa huɗu ga faɗuwar farashin man fetur.

Idan ba a sake duba kuɗin ba, kamfanin CCECC da ya daina aiki, saboda kuɗin da aka ba shi a 2013 da 2019 ba zai iya sayen kayan aikin 2025 ba.

Bayan sake dubawa na FEC na N66.115 Biliyan, daga baya ma’aikatar ayyuka ta sake ƙara kuɗin sashi na biyu biliyan zuwa Biliyan N94.

Federal Controller of Works na Katsina, Injiniya Idris Mohammad, ya bayyana hakan a lokacin duba aikin a Janairu 2026.

Ya ce “Asalin kuɗin kwangilar biliyan N29,6 sai aka sabunta kuɗin kwangila zuwa Naira biliyan N94 mai tsawon kilomita 157.10 da ake sa ran kammalawa cikin watan Agusta shekara mai zuwa 2027.

Wannan ƙarin kuɗi shi ne ya ba kamfanin damar sayen sabbin injuna, da komawa bakin aiki. Gwamnatin Tinubu ba ta sanya kuɗi kawai ba, ta canja ingancin aikin.

Aikin yanzu ba aikin kwalta na yau da kullum ba ne. An gina shi da ƙarin hanya (Additional Carriageway):* Ana gina sabuwar hanya gaba ɗaya, da gyaran tsohuwar.Ana gyara tsohuwar hanyar ta zama sabuwa kwalta mai inganci mai ɗorewa.

Haka kuma ana gina sabbin gadoji biyar a kan hanyar da samar da kankare a gefe da tsakiyar hanya na siminti mai ƙarfe, wanda zai sa hanyar ta ɗauki shekaru 50 ba tare da lalacewa ba.

A lokacin duba aikin, jami’an NSE da COREN sun tabbatar da cewa ingancin aikin da CCECC ke yi ya cika ƙa’idojin na’aikatar ayyuka.

A kasafin 2026 da Tinubu ya gabatar wa majalisar dokoki, an sake sanya Naira biliyan 76.3 a aikin hanyar Kano zuwa Katsina.

Wannan yana cikin kasafin N3.23 Tiriliyan da Gwamnatin Tinubu ta tanada don hanyoyin Tarayya baki ɗaya a 2026 — wanda ya ninka na 2024 da kusan 489%.

Wannan ya nuna cewa Tinubu ya sanya hanyar Kano — Katsina a cikin manyan hanyoyin da ya ba fifiko a Arewa.

Baya ga babban aikin tagwayen hanyoyi, Gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da shirin 260 Emergency Road Projects a faɗin Najeriya.

A cikin waɗannan 260, Arewa Maso Yamma ta fi kowa samu 48 daga ciki.

A Katsina, cikin waɗannan ayyukan gaggawa an gyara 2.4km a Mararrabar Kankara, an gyara 1.4km a Muduru, hanyar Katsina zuwa Daura.

Waɗannan ayyukan gaggawa sun buɗe hanyoyin da ambaliya ta rufe, sun sauƙaƙa wa manoma da ‘yan kasuwa. Duk da a ƙoƙarin ganin cigaba da aikin ya kankama,Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Abdullahi Tanko-Yakasai, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Hulɗa da Al’umma, ta ziyarci aikin Kano — Katsina.Tawagar ta haɗa da NSE (Nigerian Society of Engineers- COREN (Council for the Regulation of Engineering)’Yan jarida ƙungiyoyin farar hula.

Sun duba aikin, sun auna inganci, sun yi magana da kamfanin CCECC.

Yakasai ya ce:

“Tare da shigar da shugaban ƙasa ta hanyar sanya kuɗi, muna da yaƙinin wannan aikin zai yi sauri zuwa kammalawa. Matsala ɗaya kacal da muka gani ita ce batun diyya.”

Wannan tsarin sa ido ya sa kamfanin ya san cewa ana kallon aikinsa, kuma ya sa aikin ya yi sauri daga 7% zuwa 27%.

A baya kafin Tinubu, aikin ya yi sanyi, kamfani na ƙorafin rashin kuɗi
Yanzu (Janairu 2026) aikin ya kai kaso 27.04%, an gina kilomita 27 na hanya.

Shugaban kula da ayyuka na CCECC, Mr. Tang Ying, ya tabbatar da cewa aikin yana tafiya cikin sauri yanzu, kuma ya yabi Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Katsina da al’ummomin da hanyar ta ratsa.

Matsalar itace duk da gudummawar Tinubu, akwai kalubale ɗaya da ya rage: biyan diyya.

An canja tsari — yanzu Jiha ma sai ta shiga biyan diyya ga bishiyoyin tattalin arziki da gine-ginen da hanyar ta shafa. Tun da aikin ya fara kafin Tinubu, akwai ruɗani kan wane ne zai biya.

Federal Controller ya ce “Ana buƙatar Gwamnatin Jiha ta biya diyya ga bishiyoyi da gine-gine da ke kan hanyar, domin kamfani ya iya haɗa garuruwa da ƙauyuka da ke kan hanyar.

Domin haka gwamnati ba ta yi watsi da aikin da ta gada bata sanya N120 Biliyan a 2024 da 2025 ta sake duba kuɗin kwangila zuwa N134 Biliyan a FEC
Ta ƙara kuɗin sashi II zuwa N94.15 Biliyan, ta sanya N76.3 Biliyan a kasafin 2026 ta canja ingancin aiki zuwa siminti mai ɗorewa na shekaru 50.
Ta ƙaddamar da ayyukan gaggawa 48 a Arewa Maso Yamma ta kafa tsarin sa ido kai tsaye ta NSE da COREN*

Jimillar kuɗin da Tinubu ya sanya don wannan hanya kaɗai ya wuce Naira Biliyan 270 a cikin kasafin kuɗi 3 (2024, 2025, 2026).

Wannan shi ne dalilin da ya sa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya yabi Tinubu a watan Oktoba 2026, yana cewa:

“Ayyuka da yawa da gwamnatocin baya suka fara amma ba su kammala ba, da zuwan Shugaba Tinubu, yanzu sun fara ganin haske.”

Hanyar Kano — Katsina ba ta kammala ba tukuna. Amma a karon farko cikin shekaru 13, tana da kuɗi, tana da kamfani a girke, tana da inganci, kuma tana da ranar kammalawa: 21 ga Agusta, 2027.

By ukarofi

Leave a Reply