Shirin auren marayu a ƙananan hukumomin Argungu da Augie ya kankama

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirin sa na tallafa wa marayu da marasa galihu, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Argungu da Augie a zauren majalisar tarayya ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Honarabul Sani Yakubu Noma (Yar Giwa) ya bayyana cewa ba da daɗewa ba za a gudanar da auren marayu 200.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa in Sha Allahu ba da daɗewa ba za a gudanar da auren marayu 200 tare da samar musu kayan sana’o’i daban-daban domin su tsaya da ƙafafuwan su bayan an yi auren, saboda yanzu lokaci ya wuce da mace za ta zauna gidan miji ta rungume hannu tana jiran sai ya kawo mata komai na hidimar iyali, yana da kyau ita ma ta bayar da na ta gudummawar.

Yanzu haka kwamitin da aka naɗa don gudanar da shirye-shiryen auren yana nan yana tantance marayun da aka kawo sunayen su daga mazaɓu daban-daban daga ƙananan hukumomin Argungu da Augie domin kai su asibiti a yi gwajin jini da kuma awon cutukkan da ke iya zama barazana ga zamantakewa bayan aure.

Ya ƙara da cewa duk da ya ke tun shekaru uku da suka wuce ba a saka hannu a kasafin kuɗin ƙasa ba amma dai daga cikin abinda ya sauwaƙa akwai gado da kujeru da kayan aikin gida da kuma teloli da firjin-firjin ga kowace amarya wanda in sha Allahu kowace za ta sami ɗaya daga cikin kayan sana’o’i.

Honarabul Yar Giwa ya bayyana cewa taimaka wa rayuwa ba ƙaramin alkhairi ba ba ne ballanatana ma marayu wanda kuma ya fito daga gidan marasa ƙarfi.
Ya kuma nemi duk waɗanda Allah ya sa suka sami shiga cikin wannan auren da su ji tsoron Allah su riƙe mazajen su da kyau su yi amfani da duk abinda suka samu na sana’a wajen tafiyar da cigaban gidajen su.

Ya kuma yi kira ga yan kwamitin da aka naɗa da suma su ji tsoron Allah wajen aiwatar da ayyukan da aka ɗora musu musamman wajen tantance ainihin marayu mabuƙata.

By ukarofi

Leave a Reply