Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta sanar da haramta wa ‘yan mata fita sayar da kaya da dare a faɗin jihar, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 10:00.
Kwamandan Janar na hukumar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ya sanar da haka a taron manema labarai da ya kira a hedikwatar hukumar da ke Katsina.
Ya ce an ɗauki matakin ne don kare ‘yan mata daga haɗarin zamantakewa da kuma inganta bin koyarwar addinin Musulunci.
Sheikh Saifullahi ya bayyana cewa umarnin ya shafi duk wuraren da ake sayar da kaya da dare, ciki har da kasuwanni,tashoshin mota,wajen taruka da sauran su.
Ya ce jami’an Hisbah za a tura su a waɗannan wurare don sa ido da tabbatar da bin umarnin, kuma duk wanda ya karya doka za a ɗauki mataki a kansa.
Saifullahi ya bayyana cewa Hukumar ta samu rahotanni da dama da ke nuna cewa wasu ‘yan mata da ke fita sayar da kaya da daddare suna fuskantar abubuwa masu haɗari “Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin waɗannan ‘yan matan suna shiga ayyukan da ba su dace ba, wasu ana yi musu fyaɗe, wasu kuma suna aikata zina. Waɗannan ayyuka sun saɓa wa koyarwar Musulunci, kuma ba za mu bar su su ci gaba da aikata haka ba.
Ya ce wasu daga cikin ‘yan matan ba laifinsu ba ne, illa dai rashin kulawar iyaye da kuma barin su su fita da dare ya jefa su cikin haɗari.
Ya ce Hisbah ba za ta zauna ta kalli ‘ya’yan jama’a suna lalacewa ba.
Sheikh Saifullahi ya gargaɗi iyaye da su daina barin ‘ya’yansu, musamman ‘yan mata, su fita sayar da kaya a lokutan dare.
“Iyaye su ba da fifiko ga tsaro da walwalar ‘ya’yansu fiye da kuɗin da za a samu daga sayar da kaya da dare. Kuɗin dare ɗaya ba zai kai darajar mutuncin ‘ya ba.”yace.
Shugaban hukumar ya ce iyayen da suka ci gaba da barin ‘ya’yansu su fita da dare, hukumar za ta ɗauki mataki a kansu.
Baya ga batun sayar da kaya da dare, Kwamandan Janar ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ƙara sa ido kan masu sayar da magungunan gargajiya a faɗin jihar.
Ya ce an samu rahotannin cewa wasu daga cikin masu magungunan suna amfani da kalaman batsa da maganganu marasa kamala don jawo hankalin abokan ciniki.
“Amfani da kalaman batsa don jawo abokan ciniki ba za lamunta ba. Magani aikin alheri ne, ba aikin batsa ba.”
Ya ce duk wanda aka kama yana amfani da irin waɗannan kalamai, za a hukunta shi.
Kwamandan Janar ya kuma nuna takaicin sa kan rahotannin sake buɗe gidajen karuwai a wasu sassan jihar.
Ya umarci masu gudanar da gidajen da su rufe su nan take, ko kuma su fuskanci sakamakon doka.
Ya kuma sake tabbatar da cewa haramcin sayar da giya, yana nan daram a Jihar Katsina.
Ya gargaɗi waɗanda ke sana’ar sayar da giya da su daina sayar da ita a wuraren jama’a, domin hukumar ba za ta yi musu kyakkyawan fata ba.
Sheikh Saifullahi ya yi kira ga jama’a da su ba da goyon baya da haɗin kai ga hukumar.
Ya jaddada cewa an kafa hukumar Hisbah ba don tsoratar da mazauna ba ko zaluntar su, amma don tabbatar da bin dokar da ta kafa ta.
“Hisbah an kafa ta ne don gyara, ba don cutarwa ba. Muna son Katsina ta zama jihar da ake alfahari da ita wajen ɗabi’a da addini.”
Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin iyakokin dokar da ta kafa ta, tare da inganta ɗabi’un kirki a faɗin Jihar Katsina.
