Gwamna Abba ne gatan APC a Kano — Hon. Sammani Zango

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon. Sammani Muhammad Zango, shugaban dattawa na Jam’iyyar APC a ƙaramar Hukumar Ungogo, ya bayyana cewa irin ayyukan ci gaba da bunƙasa Kano da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, yake gudanarwa a fannoni daban-daban, kamar ilimi, kasuwanci, noma, kiwon lafiya, tsaro, hanyoyi, haskaka gari da samar da ayyukan yi ga dubban matasa, su ne suka sa APC ta samu gata ta fara cin zaɓe a Dawakin Kudu da Warawa na ɗan Majalisar Wakilai da aka gudanar a wannan shekarar ta 2026 a Kano.

Sammani Zango ya bayyana hakan ne lokacin da ayarin dattawan Jam’iyyar APC na mazabar ƙaro, a ƙaramar Hukumar Ungogo, suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Kano a ranar Alhamis da ta gabata, ƙarƙashin jagorancin Hon. Badamasi, sakataren Jam’iyyar APC na mazabar ƙaro.

Haka kuma, Zango ya yi kira ga al’ummar Kano da Nijeriya baki ɗaya da su sanya ƙasa cikin addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma samun ƙaruwar arziki, ta hanyar marawa shugabanni baya wajen ganin an samu ci gaba mai ma’ana a kowane lokaci.

A ƙarshe, ya ce Jam’iyyar APC ta himmatu wajen gudanar da ayyukan ci gaba, wanda hakan zai taimaka mata a zaɓukan da za a gudanar a shekarar 2027 mai zuwa a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma nemi al’umma da su ci gaba da addu’ar Allah Ya cika burin shugaban ƙasa na bunƙasa tsaron Nijeriya da tattalin arzikinta.

By ukarofi

Leave a Reply