Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
DSS ta daƙile wani babban shirin ta’addanci bayan jami’anta sun kama makamai da alburusai masu yawa da aka yi safararsu zuwa Nijeriya daga Jamhuriyar Nijar.
Makamai da aka kama sun haɗa da bindigogin AK-47 guda 21, bindigogin sarrafa kansu na PKT guda huɗu da kuma kwalaben alburusai guda 825. Jami’an DSS sun kama makaman ne a Dawakawa, ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto, bayan sanya ido kan wasu ƙungiyoyin ta’addanci da ake zargin suna ƙoƙarin shigar da makamai cikin Nijeriya gabanin zaɓen shekarar 2027.
Wata majiya mai tushe a harkokin tsaro ta bayyana cewa, sakamakon ƙara yawaitar kama makamai ba bisa ƙa’ida ba da DSS ke yi a faɗin ƙasar, ƙungiyoyin ta’addanci sun koma amfani da mata da dabbobi masu ɗaukar kaya, musamman raƙuma, wajen safarar makamai.
Majiyar ta ƙara da cewa hukumar ta gano wani kwamandan mayakan da aka ɗora wa alhakin haddasa tashin hankali kafin zaɓe da kuma lokacin gudanar da shi.
A farkon makon nan ma, jami’an DSS sun kama wata mata da ake zargi da safarar makamai mai suna Hafsat Umar a ƙaramar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara.
An kama Umar ne tare da gurneti guda 12 da bel na alburusai guda biyu. Ita ce mace ta 14 da DSS ta kama bisa zargin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba tsakanin watan Fabrairun 2025 da Nuwamban 2026.
Bayanan sirri sun nuna cewa wadda ake zargin ta je Jihar Neja ne domin samo alburusai da za ta kai wa wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Saidu Marafa, da ke Kani Kawa, ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
An gudanar da kamen matan da ake zargi da safarar makamai a jihohin Zamfara, Nasarawa, Ebonyi, Taraba, Kaduna da Filato.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai Aisha Mohammed, wadda jami’an tsaro suka cafke a watan da ya gabata a Keffi, Jihar Nasarawa, bisa zargin safarar makamai da alburusai ta hannun wani fitaccen dillalin makamai kuma mai garkuwa da mutane da aka bayyana da suna Sani. An samu alburusai 7.62mm na AK-47 guda 202 da kuma magazin guda uku marasa alburusai a wurinta.
A watan Satumban 2026, an kama wasu mata biyu, Chika Aguzie da Blessing Nwamba, a wurare daban-daban a Jihar Ebonyi bisa zargin hannu wajen samar da makamai da abubuwan fashewa ga kwamandojin haramtacciyar ƙungiyar Eastern Security Network (ESN), ciki har da Chinonso Amobi Okafor, wanda aka fi sani da Temple, da B44, waɗanda rahotanni suka ce suna da sansani a Jihar Anambra. An gano nade-naden abubuwan tayar da bama-bamai guda 14 a wurin.
A watan Agusta, DSS ta kama Rabiatu Halidu a kan titin Abacha, ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, tare da alburusai 7.62mm guda 501.
A watan Fabrairu kuma, jami’an hukumar sun kama Aisha Ibrahim a ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, tare da alburusai guda 975.
A watan Janairu, an kama Sakina Muhammad da Badariyya Abubakar a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo ta Jihar Taraba. An same su da bindigar AK-47 guda ɗaya, alburusai na musamman guda 984, alburusai na GPMG guda 105 da kuma magazin guda 14 marasa alburusai.
Hukumar ta kuma samu nasarar kama wasu mata a shekarar 2025, ciki har da Rahane Sanusi a ƙaramar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara, lokacin da take safarar alburusai daga hannun wani dillalin makamai ba bisa ƙa’ida ba a Sokoto zuwa ga wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Ibrahim Bare, wanda aka fi sani da Baba, a ƙaramar Hukumar Anka.
Sauran matan da aka kama sun haɗa da Suwaiba Abubakar, Halima Umar, Firdausi Haruna, Saidya Ibrahim da Fatima Sani, inda aka samu makamai da alburusai masu yawa a wurinsu.
A farkon wannan shekarar, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mata hukunci a shari’o’in da suka shafi ta’addanci, waɗanda suka shafi mata da aka kama bisa zargin safarar makamai. A wasu shari’o’i biyu, an yanke wa mata uku, Halima Abdullahi, Safiya Salihu da Halima Umar, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari kowannensu.
Wata majiya a fannin tsaro ta ce, kamar sauran waɗanda aka kama a baya, za a gurfanar da Hafsat Umar a gaban kotu, yayin da DSS za ta yi amfani da bayanan sirrin da take da su wajen kamo sauran masu aikata laifuka.
Majiyar ta ƙara da cewa DSS za ta ci gaba da amfani da sahihan bayanan sirri da kuma ayyukan tsaro domin gano tare da kama dukkan waɗanda ke da hannu a safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
