Hon. Kundu ya yaba wa Gwamna Namadi kan gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Jigawa

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Kwadinetan ƙungiyar The Game Changer Group (TGCG) kuma Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, Hon. Bashir Kundu, ya yaba wa Gwamna Malam Umar Namadi da mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na APC a jihar bisa abin da ya bayyana a matsayin nasarar da aka samu wajen shirya gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026.

Hon. Kundu ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan yadda aka gudanar da gangamin, wanda ya samu halartar dubban magoya baya da mambobin jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na jihar. An gudanar da taron ne a filin wasa na Dutse Township Stadium, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen wayar da kan jama’a da neman goyon baya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya musamman yaba wa Gwamna Namadi da sauran mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen bisa ƙoƙarinsu, haɗin kai da jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar shirya gangamin. A cewarsa, yawan mutanen da suka halarci taron ya nuna irin shiri da ƙoƙarin tattara magoya bayan da shugabancin jihar da masu shirya gangamin suka yi.

Kundu ya ce, “Ina miƙa yabo na musamman ga Mai Girma Gwamna Malam Umar Namadi da dukkan mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa bisa nasarar shirya wannan gangami. Tsarin shirya taron, haɗin kai da ƙoƙarin tattara jama’a abin a yaba ne. Tattaro dubban magoya baya a Dutse ya nuna irin ƙoƙarin da aka yi wajen ganin taron ya gudana cikin nasara,” inji shi.

Hon. Bashir Kundun ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa kan ƙarfin siyasar APC a Jihar Jigawa, inda ya ce jam’iyyar ce ke da rinjaye a harkokin siyasa a jihar. Ya bayyana cewa, a ganinsa, a halin yanzu babu wata jam’iyyar siyasa da ke gudanar da harkokin siyasa da tattara magoya baya kamar yadda APC ke yi a Jigawa.

“A halin yanzu, babu wata jam’iyyar siyasa da ke yin motsin siyasa a Jihar Jigawa kamar APC. Jam’iyyarmu tana da tsare-tsare da rassa a faɗin jihar, don haka wajibi ne mu ci gaba da ƙarfafa su yayin da muke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027,” inji Kundu.

Haka kuma, ya yi kira ga mazauna jihar da magoya bayan jam’iyyar da su kula da katunan zaɓensu na dindindin (PɓC), tare da tabbatar da cewa sun tanadi kansu domin shiga zaɓe mai zuwa. Ya buƙaci su yi amfani da damar da suke da ita ta hanyar zaɓe wajen marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC da za su tsaya takara a matakan tarayya, jiha da majalisun dokoki baya.

“Ina kira ga al’ummarmu da su adana katunan zaɓensu yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa sun shirya kaɗa ƙuri’unsu idan lokacin zaɓe ya yi. Shigarsu zaɓe na da matuƙar muhimmanci. Ya kamata dukkanmu mu kasance cikin shiri domin fito wa mu zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC a dukkan matakai a zaɓen 2027,” ya ƙara da cewa.

Hon. Kundu ya kuma yi tsokaci kan gudunmawar da ƙungiyar The Game Changer Group ta bayar a lokacin gangamin, inda ya bayyana cewa reshen ƙungiyar na Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancinsa, ya halarci taron tare da sauran masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar.

Ya ce halartar TGCG wani ɓangare ne na gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa wajen shiga harkokin siyasa da ayyukan da suka shafi yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar.

A ƙarshe, ya sake jaddada aniyar reshen TGCG na Jihar Jigawa ta ci gaba da aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki, tare da gudanar da ayyukanta ta hanyar tsare-tsare da rassanta da ke faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply