Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Sashen kula da ɗakin karatun kimiyya da sadarwa na Jami’ar Bayero, Kano (BUK), ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Haruna Musa, ya shirya taron ƙasa domin tattauna ƙalubale da matsalolin da fannin kula da ɗakunan karatu ke fuskanta a duniya sakamakon shigowar fasahohin AI da ICT da sauran su.
Wannan ya sa aka gayyaci masana da masu ruwa da tsaki domin fuskantar ƙalubalen da wannan fanni ke fuskanta, tare da duba tasirinsa a sauran fannoni na ilimi da rayuwa baki ɗaya, kamar yadda shugabar ƙaramin kwamitin shirya taron, LOC, Dakta Binta Ladon Faruk, ta bayyana a wajen taron ƙasa da aka gudanar a sabon harabar Jami’ar Bayero da ke Kano, a ranar Litinin ɗin nan.
Tun da farko, a jawabinsa, mataimakin shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, ya ce an gayyato masana da shugabannin jami’o’i daban-daban na ƙasar nan, da shugabannin manyan makarantu, shugabannin ɗakunan karatunsu da sauran masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin tinkarar waɗannan ƙalubale da magance matsalolin da wannan fanni ke fuskanta a wannan zamani.
A ƙarshe, ya yaba wa shugabannin wannan sashe da sauran waɗanda suka taimaka wajen shirya taron ƙasa domin tattauna ƙalubalen da ke fuskantar fannin kula da ɗakunan karatun kimiyya da sadarwa a wannan zamani.
