Sanatoci sun yi barazanar gayyatar kamfanonin sadarwa da minista kan matsalar ‘network’

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi barazanar gayyatar Ministan Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, da kuma kamfanonin sadarwa domin su yi bayani kan matsalar ƙarancin ingancin sadarwa da kuma cire kuɗin kati ba bisa ƙa’ida ba.

Barazanar ta biyo bayan amincewar majalisar da wani ƙuduri a zaman ta na ranar Laraba, inda aka nuna damuwa kan asarar kuɗaɗen da ’yan Nijeriya ke yi sakamakon katsewar kira, rashin samun damar haɗa kira da sauran matsalolin sadarwa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Kwamitin Majalisar kan Sadarwa zai fara tattaunawa da Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya (NCC), domin neman ƙarin bayani kan korafe-korafen da masu amfani da layukan sadarwa ke yi.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa idan bayanan da hukumar ta bayar ba su gamsar da majalisar ba, za ta gayyaci ministan, Mataimakin Shugaban Hukumar NCC da kuma kamfanonin sadarwa domin yi musu tambayoyi.

Akpabio ya zargi ƙarancin sa ido daga hukumomin da ke kula da harkokin sadarwa da kasancewa ɗaya daga cikin abubuwan da ke haddasa asarar kuɗaɗen da masu amfani da layuka ke yi, yana mai cewa majalisar za ta ɗauki ƙarin matakai idan ba a samu gyara ba.

ƙudurin, wanda Sanata Tahir Monguno ya gabatar, kuma Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Oyelola Ashiru, ya karanta, ya jawo hankali kan yawaitar korafe-korafen masu amfani da layukan waya da ke rasa kuɗin kati duk da cewa ba a samu nasarar kiran da suka yi ba.

Sanata Monguno ya bayyana cewa ’yan Nijeriya na yawan fuskantar matsalolin haɗa kira, katsewar kira ba zato ba tsammani, rashin jin muryar wanda ake magana da shi da kuma tangardar sadarwa, lamarin da ke tilasta musu sake yin kira tare da kashe ƙarin kuɗi.

Ya ce bai kamata a riƙa cire wa masu amfani da layukan waya kuɗi kan ayyukan da kamfanonin sadarwa suka gaza samar musu yadda ya kamata ba.

Sanatan ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta umarci Kwamitinta kan Sadarwa ya tattauna da NCC da kamfanonin sadarwa domin gudanar da bincike kan korafe-korafen, tare da ba da shawarwarin matakan da za su kare haƙƙin masu amfani da layukan sadarwa.

Sai dai Sanata Akpabio ya bayyana cewa wa’adin makonni huɗu da kwamitin ya buƙata domin gabatar da rahotonsa ya yi tsawo, duba da gaggawar da matsalar ke buƙata.

By ukarofi

Leave a Reply