Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina za ta gina asibitin dabbobi na zamani na farko domin bunƙasa harkokin kiwo da inganta lafiyar dabbobi musamman don samun ingantaccen nama a ciki da wajen jihar Katsina.
Kwamishinan yaɗa labarai Dr Bala Zango ya sanar da haka ga manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa na karo 19 ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Malam Dikko Raɗɗa inda ta amince da aiwatar da mahimman ayyuka a jihar.
Majalisar ta kuma amince da gyaran yaran makarantun sakandare guda 19 da aka zaɓa a faɗin jihar, bisa buƙatun da al’umma suka gabatar yayin tarukan tattara bayanan kasafin kuɗi a mazaɓu 361 na faɗin jihar.
Duk a zaman majalisar, ta amince da biyan diyya ga masu kadarori su 364 da aikin gina hanyar Rahamawa zuwa Abattoir a cikin birnin Katsina ya shafa.
Gwamnatin Jihar za ta rage kuɗaɗen rajista, lasisi da sabunta lasisi na shekara-shekara ga masu sana’ar saye da sayar da kayan gwangwan da ƙarafa da sauran makamantansu.
Majalisar ta amince wa gwamnati da ta ɗaga matsayin cibiyar Cancer da Imaging Center da ake ginawa a babban asibitin ƙwararru na Janar Amadi Rimi, zuwa cibiyar kula da cututtuka na musamman da ciwon daji (Specialty Hospital).
Haka kuma gwamnatin Katsina za ta gina titi a Ɗanmusa da wasu hanyoyin cikin gari, da kuma hanyar Dutsinma zuwa Wakaji har zuwa Karofi.
Sauran ayyukan da majalisar zartarwa ta amince da su sun haɗa da gyaran Bankin Ajiya da Lamuni na Jihar Katsina (Amana Microfinance Bank) da ke shiyyoyin Katsina, Funtua da Daura, domin inganta ayyukansu ga al’umma.
Da Fitar da kuɗi har Naira biliyan 5.713 domin gudanar da kashi na farko na Shirin NG-CARES, wanda aka tsara domin tallafa wa fannoni daban-daban na tattalin arziki.
