Mambobin APC a Jos sun jaddada goyon bayansu ga tazarcen Tinubu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, Jos

Dafifin magoya bayan jam’iyyar APC ne daga ciki da wajen Jihar Filato suka halarci taron gangamin yaƙin neman sake zaɓen Shugaban ƙasa Bola Tinubu, a yayin babban zaɓen shekarar 2027, wanda ake gudanarwa a babban filin wasa na Jos da ke hanyar Zariya.

A yayin haɗa wannan rahoto dai jama’a na ta tururuwa zuwa dandalin taron yayin da masu gabatar da jawabai da mawaƙa ke cigaba da nishaɗantar da jama’a, da ƙara tayar musu da tsimin kishin jam’iyya. Yayin da ake cigaba da dakon isowar shugaban ƙasa, wanda yake gudanar da wasu ayyuka da Gwamna Caleb Mutfwang ya gudanar da suka haɗa da motocin sufuri a ƙananan hukumomi, da kuma cibiyar sarrafa na’urar kwamfiyuta da samar da ayyukan yi ga matasa.

Tun a jajiberen wannan babban taro, tawagar jami’an gwamnati da Jam’iyyar APC suke ta isa Jos babban birnin Jihar Filato, don halartar wannan taro, ciki har da Babban Hadimin Shugaban ƙasa kan harkokin watsa labarai, Abdul’Azeez Abdul’Azeez, wanda ya yi wata ganawa da manema labarai da ke aiki kan ziyarar shugaban ƙasar. Ya yi kira ga manema labarai su bayar da rahotannin abubuwan da ke faruwa yadda za su ilimantar da jama’a kan ayyukan shugaban ƙasa da gwamnatin jihar Filato, ba tare da sanya son zuciya ko ɓoye gaskiya ba. Akwai kuma tawaga ta musamman ƙarƙashin ƙungiyar City Boy Movement wacce ɗan shugaban ƙasa Seyi Tinubu ke jagorantar.

Babban Daraktan ƙungiyar City Boy a Jihar Filato, David Daser, ya buƙaci matasa su ba da haɗin kai da goyon baya, don samun nasarar wannan babban taro, da kuma shiga ƙauyuka da lunguna don gabatar da musu manufofin Shugaba Tinubu da ayyukan da ya gudanar, don sake samun amincewarsu a zaɓen 2027.

A cewar Daraktan Kula da Ma’aikata a Cibiyar Progressives Institute da ke Abuja, Idris Salihu Kwando, jama’ar Jihar Filato masoyan APC ne da shugaba Tinubu, kuma babu shakka a shirye suke su ba shi dukkan goyon da yake buƙata, don ya kai Nijeriya ga sauyin da kowa yake muradi.

Alhaji Idris Kwando wanda jigo ne a Jam’iyyar APC a Jihar Filato, shi ne kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Filato, ya bayyana ƙwarin gwiwar sa kan samun nasarar Jam’iyyar APC a matakin ƙasa da jihohin Nijeriya ba tare da samun wata hamayya ba. A cewarsa, ayyukan da Jam’iyyar APC ta yi na cigaba a Nijeriya a bayyane suke, kuma al’ummar Filato sun ji daɗin wannan gwamnati fiye da ko’ina a arewacin ƙasar nan.

Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman zaɓen Shugaban Ƙasa a Birane da Ƙauyuka, Shehu Bala Usman, ya jaddada cewa Jam’iyyar APC a Jihar Filato ta yi dukkan shirin da ya kamata don yi wa shugaban ƙasa kyakkyawar tarba, da tarin ƙuri’u masu yawa a Babban Zaɓe mai zuwa, a 2027.

Ya ce, “Jihar Filato ita ce jihar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, don haka dole ne namu tsarin ya sha bamban, kuma daga yanzu har zuwa ranar ba zamu huta ba. Za mu cigaba da yaƙin neman zaɓe har sai APC ta samu nasara a dukkan matakai.”

Ya ce, gwamnatin tarayya ta ware kuɗaɗe masu yawa, don tallafawa rayuwar mata da matasa, musamman waɗanda rikice-rikice suka kassara. Gwamnatin Tarayya ta ɗauki batun tsaro da zaman lafiyar al’ummar Filato da muhimmanci sosai, kuma hakan ya kawo cigaba da lafawar ayyukan ýan ta’adda da ɓatagari. Ga hanya mai nisan kilo kilomita 700 daga Akwanga zuwa Gombe, za ta biyo ta Jihar Filato.

By ukarofi

Leave a Reply