Talauci ke tilasta wa almajirai bara a titi – Sarkin Musulmi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya danganta yawaitar yara almajirai da ke bara a tituna da matsalar talauci, yana mai cewa mafi yawancinsu suna da sha’awar neman ilimi, sai dai rashin abin da za su dogara da shi ne ke hana su samun damar yin hakan.

Ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan magance matsalar talauci da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar. Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a birnin Gombe, yayin taron shekara-shekara na 2026 na ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Barewa (BOBA), inda ya jagoranci taron a matsayin babban baƙo.

Ya ce da dama daga cikin yaran da ake gani suna yawo a tituna suna neman abinci, ba wai don ba sa son karatu ba ne, illa talauci ne ya jefa su cikin wannan hali. A cewarsa, talauci shi ne babban abin da ke haddasa yaran fita tituna suna bara domin neman abinci, duk da cewa suna da burin zuwa makaranta, amma ba su da isassun kuɗaɗen da za su biya buƙatunsu na karatu. Ya jaddada cewa addinin Musulunci bai amince da bara ba, don haka wajibi ne kowa ya tashi tsaye wajen yaƙi da wannan ɗabi’a.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a matsayin babbar matsala da ke da illa ga tsaron ƙasa da kuma ci gabanta. Ya ce ilimi yana da matuƙar muhimmanci a koyarwar addinin Musulunci, don haka bai kamata a yi watsi da shi ba saboda halin tattalin arzikin iyayen yaro. Ya bayyana cewa ilimi shi ne ginshiƙi da tubalin addinin Musulunci, domin mutum na buƙatar ilimi ko wajen gudanar da ibadarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, wanda ya halicce shi domin ya bauta Masa.

Haka kuma, ya yi watsi da iƙirarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na cewa Musulmi ba sa son yaransu su yi karatun boko, yana mai jaddada cewa karatun addini da na zamani dukkansu suna da muhimmanci. Sarkin Musulmin ya buƙaci gwamnatoci da su samar da arin damammaki ga yaran da ke cikin mawuyacin hali, domin su samu damar zuwa makaranta, koyon sana’o’in dogaro da kai da kuma zama ’yan ƙasa masu amfani ga al’umma.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Gombe bisa kafa makarantar da yara almajirai za su riƙa haɗa karatun Alƙur’ani da karatun boko, tare da koyon sana’o’i daban-daban. Ya kuma kawo misalin irin wannan shiri da ake gudanarwa a Jihar Zamfara, inda ya buƙaci sauran jihohi su yi koyi da su ta hanyar kafa cibiyoyi da za su taimaka wajen ɗaukar yaran da ba su da damar samun ilimin boko.

Sai dai Sarkin Musulmin ya bayyana cewa matakan da ake ɗauka a halin yanzu ba su wadatar ba idan aka yi la’akari da girman matsalar, don haka ya yi kira da a gaggauta ɗaukar ƙarin matakai domin shawo kanta. Ya kuma bayyana cewa ana ƙoƙarin bunƙasa ilimin ’ya’ya mata ta hanyar wani shiri mai suna Keeping Girls in School (Shirin Tabbatar da ’Ya’ya Mata Sun Ci Gaba da Karatu), wanda ya ce an samu gagarumin ci gaba a cikinsa.

Da yake tsokaci kan taron tsofaffin ɗaliban makarantar Barewa, Sarkin Musulmin ya bayyana taron a matsayin wata dama da ke bai wa waɗanda suka yi karatu a makarantar damar sake haɗuwa, ƙarfafa zumunci da bunƙasa dangantakarsu. Ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su tabbatar da cewa zumuncin da ke tsakaninsu bai tsaya ga tarukan sada zumunta kawai ba, su riƙa taimaka wa juna musamman a lokutan ƙunci da buƙata.

By ukarofi

Leave a Reply