
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargin ‘yan daba ne, sun ƙaddamar da farmaki akan ayarin motocin tsohon Gwamnan Jihar Kano Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, a lokacin da suka kai ziyarar yaƙin neman zaɓe a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke jihar.
Kakakin ɗan takarar gwamnan, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga ‘yan jarida, inda ya ce maharan sun raunata wasu mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen da lalata motocinsu.
A cewarsa, da fari tawagar ta kai ziyara ne zuwa ƙananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Ɓagwai cikin nasara ba tare sa fuskantar wani hargitsi ba. Daga bisani an sanar da tawagar cewa wasu mutane da ke adawa da yaƙin neman zaɓen sun tare hanyar zuwa yankin Bichi.
Ya bayyana cewa, a yayin da suka isa Bichi, mambobin tawagar sun fuskanci ana harbe-harbe da duwarwatsu, amma duk da haka suka yi ƙoƙarin zuwa sakatariyar ƙaramar hukumar. Jim-kaɗan bayan wucewa ta sakatariyar ne sai wasu fusatattun matasa ɗauke da makamai suka bayyana tare da ƙaddamar da hari kan ayarin.
Shu’aibu ya kuma yi zargin cewa maharan sun casa mambobin kamfe ɗin, lamarin da ya haifar da jikkata wasu da lalata motoci a lokacin. Ya ce, ya gano cewa kusan motoci bakwai aka farfasa wa gilasai da lalata wasu sassansu.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wani saƙo a kai ba.

