Tinubu ya ƙaddamar da shirin tsaron shekara biyar don kawo ƙarshen rashin tsaron shekaru 17

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ƙaddamar da Shirin Dabarar Ayyukan Tsaro na Shekara Biyar da nufin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro na tsawon shekaru 17 da ya addabi wasu sassan Nijeriya ta hanyar ƙarfafa wa lamuran tsaro, inganta ƙoƙarin sojoji da shirya wa tunkarar barazanar tsaro masu tasowa. An shirya wannan tsari ne domin ya dace da ababen da ayyukan tsaron Nijeriya suka fi fifitawa, samar da ababen da ake buƙata, ci-gaban ƙarfi, da kashe-kashe da hauhawarsa da kuma fuskantar ƙalubalen tsaro.

Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, Dele Alake ne ya bayyana wannan shiri a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da Shugaba Tinubu yake yi wajen daidaita al’amuran tsaron Nijeriya a zamanance ta yadda zai iya fuskantar dukkan wasu nau’ukan barazanar tsaro da suka haɗa da tayar da ƙayar baya, ayyukan ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da wasu ayyukan ta’addanci a ƙasar.

A cewar sanarwar, ayyukan sojoji a tsawon shekaru uku da suka gabata, sun yi sanadiyyar halaka sama da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga 15,000, yayin da sama da mayaƙan Boko Haram da iyalansu guda 130,000 ne suka miƙa wuya ta atisayen Operation Safe Corridor, wato shirin Gwamnatin Tarayya na gyaran hali ga tubabbun mayaƙan ‘yan ta’adda. Ya ce, hakan nasara ce da aka samu ƙarƙashin shirin bin hanyoyi biyu wajen daƙile ayyukan ta’addanci da suka ƙunshi atisayen sojoji da tattaunawar sulhu.

A ɓangaren ƙoƙarin ƙarfafa wa ƙarfin sojan Nijeriya da inganta harkokin daƙile barazanar tsaro, Shugaba Tinubu ya amince da samar da sababbin dibishon ɗin sojoji guda huɗu da sabunta tsare-tsaren sansanonin sojoji a faɗin ƙasar. Hakan na da nufin faɗaɗa ayyukan sojoji ta yadda za su riƙa daƙile dukkan wata barazanar tsaro kan ƙasar da al’ummarta.

Haka kuma, shugaban ya amince da kafa ƙarin defo guda biyu a garin Osogbo na Jihar Osun da Amasiri-Edda da ke Jihar Ebonyi, domin faɗaɗa fagagen horarwar sojoji da rage jinkiri wajen ɗiba da horar da sababbin sojoji. Ya ce, kowane defo zai iya ɗaukar mutum 6,000 a lokaci guda, wanda ke nuna su biyun za su iya kula da lamuran horar da sojoji 12,000. Tuni aka fara aiki da na Osogbo wanda a yanzu ana horar da sojoji 5,210 acikinsa.

Don ƙarfafa wa adadin dakarun soji, Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin sojoji guda 28,000 a faɗin Nijeriya da nufin bunƙasa ingancin ayyukan rundunar. Kazalika, Shugaban Nijeriyar ya amince da ɗaukar jami’an ‘yan sanda 50,000 a matsayin ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa wa tsaron cikin gida, faɗaɗa ƙarfin ‘yan sanda da inganta harkokin daƙile aikata miyagun laifuka.

Baya ga siyan makamai, fasaha da horo, gwamnatin jagoran jam’iyyar APCn ta kuma zuba jari a masaukin sojoji da harkokinsu don bunƙasa walwala, wuraren aiki da inganta dakaru. Daga cikin su akwai samar da barikin sojoji na Jihar Ekiti a garin Ikere-Ekiti, wanda aka samar da nufin ƙarfafa wa walwalar jami’an.

Ana sa ran wannan shiri ya inganta kimtsin dakaru, toshe dukkan wani giɓin da ake samu yayin ayyukan jami’an tsaro da tabbatar da amfani da kayayyakin da ake da su bisa inganci da kuma rage kashe-kashe da ɓarnatar da kuɗaɗe akan ababen da ba su da muhimmanci.

By Babaji

Leave a Reply