Kotun Kano ta tsare mutum biyu kan zargin fashin adaidaita sahun miliyan N3.68

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata kotu a Jihar Kano ta umarci a tsare wasu mutane biyu, Shehu Ibrahim da Abubakar Isa a gidan gyaran hali kan zargin su da hannu a kitsa makirci da aikata fashi da makami. An gurfanar da su ne a kotun bisa tuhume-tuhumen da Barista Maryam Halilu Ɗantiye ta gabatar wa kotun.

Wani jami’in kotu, Muhammad Musa Tudun-Wada, ya fassara wa mutanen tuhume-tuhumen da ake yi akansu domin tabbatar da cewa sun fahimci zarge-zargen da ake musu.

Bayan sauraron tuhume-tuhumen, kotun ta umarci a tsare mutum biyun a gidan gyaran hali har zuwa ranar 24 ga Nuwamba, 2026, a lokacin da za a sake zama kan al’amarin.

Ana zargin su ne da yin fashi ga wani ɗan adaidaita sahu mai suna Sadik Ahmad, inda suka yi masa barazanar cutar da shi da ƙwace masa adaidaita, wanda kuɗinsa ya kai kimanin Naira miliyan 3.68 da wayar hannunsa. An yi zargin cewa al’amarin ya auku ne a yankin ƙauyen Gaya da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano.

By Babaji

Leave a Reply