Daga SANI GAZAS CHINADE Damaturu
Gwamnatin Jihar Yobe ta haramta liƙa tare da baje kolin fastocin kamfen a gine-ginen gwamnati, gefen tituna da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana a faɗin jihar.
Wata sanarwa da ofishin mashawarci na musamman kan tsaro ga Gwamna Mai Mala Buni, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ya fitar, ta ce takunkumin ya shafi kusan dukkan gine-gine gwamnatin da aka sabunta da suka haɗa da filin wasa na 27 Augusta da kuma gadar sama ta zamani da aka gina a tsakiyar garin Damaturu.
A cewar sanarwar wannan umarnin yana da nufin kiyaye ababen more rayuwa na jama’a, kiyaye tsaftar muhalli da kuma kare kyawawan gine-ginen da aka gina a jihar.
Kamar yadda sanarwar ke cewa haka nan wannan haramcin ya shafi dukkan jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, magoya baya da ƙungiyoyin kamfen ba tare da wani banbanci ba.
Sanarwar ta yi gargaɗin cewa duk jam’iyyar siyasa, ɗan takara, magoyin baya ko mutumin da aka samu yana karya wannan doka zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada bisa ga dokokin da suka dace.
Don haka ta buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, magoya baya da ƙungiyoyin kamfen da su bi wannan doka sosai.
An bayar da umarnin a fara aikin tilasta dokar don cire fastocin kamfen da aka riga aka manna a gine-ginen gwamnati da sauran ababen more rayuwa na jama’a da aka haramta.
Rahoton na ƙarin haske da cewa matakin ya zo ne a dai-dai lokacin da ake nuna damuwa kan yadda ake kara ɓata gari da sauran dukiyoyin gwamnati ta hanyar manna fastocin kamfen na siyasa ba tare da sanarwa ko neman izini ba.
