Gobara ta tashi a wani gidan mai a Jega

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Da sanyin safiyar Talatar nan ne gobara ta tashi a gidan mai na AGO mallakar Alhaji Yusuf Zarummai Jega da ke kan hanyar Yauri da a garin Jega da ke jihar Kebbi.
Malam Muhammed Jafar wani da abin ya faru a gaban sa ya bayyana cewa ana cikin sauke mai daga wata babbar mota ne a gidan kawai sai wutar ta tashi kuma bayan motar ta kama da wuta daga nan wani sashe daga gidan man shi ma ya kama da wuta.
Ya ƙara da cewa duk da mutane sun yi dabubu a wajen ba wani taimako da su ke iya yi sai dai kallo daga nesa.

Babu ma’aikatan kashe gobara kuma mutane ba wanda ke iya isa wajen saboda hatsari.
Ya bayyana cewa ba a dai sami asarar rayuwa ba amma dai an tafka asara mai yawa duk da ya ke dai ma’aikatan gidan tare da taimakon waɗansu matasa sun yi ƙoƙarin fitar da kayan da su ke iya fitarwa daga ofis-ofis din da ke gidan kafin wutar ta yi kamari.
Sai dai babu wani bayani daga masu gidan man saboda kowa a rikice ya ke, haka-zalika babu wani bayani a hukumance daga hukumomin da abin ya shafa.

By ukarofi

Leave a Reply