Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A wannan mako ina so ne in mayar da hankali wajen yabawa ga irin gudunmawa da rawar ganin da mata matasa ke samu a matakai daban-daban, musamman a harkokin shugabanci da siyasa. Haka abin yake a fannonin rayuwa daban-daban, inda za ka ga mata matasa daga arewacin Nijeriya suna taka rawar ganin da kowa ke alfahari da su. Matasan mata irin su, Maryam Lawan Gwadabe, Safiyya Daba, Fatima Askira, Maryam Bukar Alhan Islam, Fatima Bala, suna ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban fasahar zamani, kasuwanci, zaman lafiya, da adabi.
Matasan mata daga sassan jihohin Arewa na nuna tsayuwar daka da jajircewa, don ganin kamar takwarorinsu maza, su ma sun yi abin wani abin bajinta, wanda jama’a za su ci moriyar sa, kuma tarihi ya tuna da su wata rana. Daga cikin irin waɗannan matasa akwai Ambasada Zainab Musa Ya’u, wata matashiya daga Jihar Gombe, wacce tauraruwar ta ke ƙara haskawa, ba ma a jihar ta ta Gombe ba, har ma da Nijeriya bakiɗaya.
Ba da jimawa ba ne aka zaɓi Zainab a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar Matasan Nijeriya, a wani babban zaɓe da aka gudanar na sabbin shugabannin majalisar. Allah ya bai wa Ambasada Zainab Musa Ya’u, wannan muƙami ne ba kawai don kasancewar ta mace kuma ’yar Arewa ba, sai don irin ƙwazo da juriya da ta kasance tana nunawa a baya; tun daga matakin jihar har zuwa tarayya.
A cikin wani yanayi mai nuna ƙarfin zuciya, iya jagoranci, da gogewa a harkar gwagwarmayar matasa, matashiyar mai riƙe da sarautar Giwar Matan Gona, ta bayyana cewa wannan nasara da ta samu ba tata ba ce kawai ta al’ummar Jihar Gombe da ƙasa bakiɗaya.
Wannan nasara wani babban mataki ne da ya yi sanadin kafuwar tarihi ga Jihar Gombe, kasancewar Zainab ta zama mutum na biyu daga jihar da ya taɓa samun wannan kujera a matakin ƙasa a Majalisar Matasan Nijeriya. Hakan ya ƙara ƙarfafa kasancewar ta wakiliyar jihar a tsarin jagorancin matasa na ƙasa.
Sakamakon wannan zaɓe ya bayyana wata muhimmiyar dama ce ta musamman da Jihar Gombe ta samu, ba kawai saboda muƙamin da Zainab ta samu ba, har ma da nauyin da ke tattare da samun wannan kujera. Kujera ce da ke wakiltar shigar matasa cikin harkokin ƙasa, wakilcin mata, da kuma ƙarin damar da ke buɗe wa matasan Nijeriya daga sassa daban-daban ƙofofi, don ba da gudunmawa ga jagorancin ƙasa da ci gaban dimokuraɗiyya.
A wajen Zainab Musa Ya’u, wannan nasara ita ce sakamakon jajircewar da ta daɗe tana nunawa mai cike da ƙarfin zuciya, juriya, da rashin nuna wariya, da kuma sadaukarwa marar iyaka yayin jagoranci da hidimar jama’a. Harkokinta na siyasa da jagoranci na cigaba da nuna sha’awarta ga ƙarfafa gwiwar matasa, mulkin haɗa kan jama’a, cigaban al’umma, da inganta mata a fagen jagoranci.
Zainab Musa Ya’u ta fito ne daga ƙaramar Hukumar Akko, da ke Jihar Gombe, tana riƙe da muƙamai daban-daban a harkokin matasa, tun daga lokacin da take karatu a Jami’ar Jihar Gombe, inda tauraruwarta ta fara haskawa a fagen jagoranci. Ta shiga ƙungiyoyin ɗalibai, na matasa, na harkokin al’umma, fafutukar samar da zaman lafiya, da ayyukan da suka shafi cigaban al’adu da masarautu. Ta cigaba da nuna sha’awar samar da wata dama da za ta ƙarfafa gwiwar matasa, musamman mata, su shiga cikin harkokin siyasa da shugabanci.
A yayin da take bayyana farin cikin ta kan nasarar da ta samu, Zainab Musa Ya’u ta nuna godiyarta ga Allah Maɗaukakin Sarki da wannan dama da ta samu, tare da bayyana cewa nasarar da ya bata, inda har ta zama wani abin tarihi ba kawai ga kanta ba, har ma ga Jihar Gombe bakiɗaya, da ma duk wani wanda ke goyon bayan ganin matasa sun samu shiga cikin harkokin jagoranci da gina ƙasa.
Ta amince kan cewa, nasarar da ta samu ba ta zo mata kawai a cikin ruwan sanyi ba, doguwar tafiya ce mai cike da ƙalubale. Sai dai a cewarta, nasara ce da ta samu sakamakon goyon baya da take samu daga iyalinta da ’yan uwanta, masu ƙarfafa mata gwiwa, addu’o’in iyaye da masoya, masu ba ta shawarwari, abokan aikinta, makusantanta, da masu goyon bayanta, duk sun taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan nasara.
Haka kuma ta bayyana godiyarta ga shugabanni da mambobin Majalisar Matasan Nijeriya, musamman waɗanda suka goyi bayan burinta a duk tsawon lokacin yaƙin neman zaɓenta.
A matsayinta na Mataimaciyar Shugaban Majalisar Matasan Nijeriya, ana sa ran Zainab za ta ba da gudummawa ga muhawara mai amfani a cikin Majalisar, ingantaccen wakilci, da kuma ƙara tattaunawa kan batutuwa masu shafar matasan Nijeriya.
Haka nan, nasararta na tura saƙo mai ƙarfafawa ga matan Nijeriya cewa ana iya bin damar jagoranci ta hanyar ƙarfin zuciya, kyakkyawan tanadi, sadaukarwa, da shiga tsakani a harkokin jama’a.
Nasarar ta ƙara buɗe sabon wani shafi a tarihin jagorancin matasa daga Jihar Gombe, kuma ta zama abin ƙarfafawa ga matasa masu burin ba da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban al’ummominsu.
Yayin da muke nuna murna da nasarar da Dakta Zainab samu zan jaddada cewa kada a ɗauki wannan nasarar a matsayin matakin ƙarshe, sai dai a matsayin mabuɗin ƙofofin alkhairai masu yawa a nan gaba.
Ga al’ummar Jihar Gombe, wannan wani lokaci ne na ƙara nuna haɗin kai da goyon baya ga wannan baiwar Allah. Ga matan Arewa da Nijeriya bakiɗaya kuwa, wannan wani kyakkyawan misali ne gare su, wanda ke nuna cewa su ma za su iya, kuma abu ne da zai iya faruwa da kowacce mace da ta nuna juriya, jajircewa da biyayya kamar yadda Zainab Musa Ya’u, ta nuna a fafutukar da take yi na samar da sabon tsarin shugabanci ga matasan Nijeriya.
Kamar Zainab da sauran matasan mata da muka ambata a baya, lallai akwai buƙatar iyaye da al’umma su riƙa tallafawa ’ya’yansu mata masu ilimi da basira wajen ganin sun cimma burikansu na rayuwa, da kuma ba da gudunmawa ga al’umma. Duk wani yunƙuri da wata matashiya ta taso da shi, matuƙar bai yi hannun riga da koyarwar addinin Musulunci da al’adun al’ummar Arewa ba to, yana da kyau a mara musu baya.
