Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani tsohon kwamishinan zaɓe, Mike Igini, ya buƙaci Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, da ya ɗauki tsauraran matakan diflomasiyya kan maguɗin zaɓe a Nijeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa Igini ya gabatar da buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 13 ga Nuwamba, 2026, wadda ya aika wa Trump a Fadar White House, inda ya ba da shawarar wata manufa da ya kira “No Mandate Fraud”, wato ƙin amincewa da shugabancin da aka samu ta hanyar maguɗin zaɓe.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta danganta hulɗar diflomasiyya da yarjejeniyoyin hulɗarta da Nijeriya da sahihancin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Igini ya bayyana cewa matsalar maguɗin zaɓe da ta daɗe tana faruwa, cin hanci da rashawa, rashin tsaro da kuma raunin tsarin ɗora wa shugabanni alhakin ayyukansu, sun rage amincewar ’yan Nijeriya ga gwamnati, tare da taimakawa wajen ƙara yawan mutanen da ke neman damar rayuwa a ƙasashen waje.
A cewarsa, magance tushen matsalar ƙaura zuwa ƙasashen waje ya wuce ɗaukar matakan tsaro a kan iyakoki, domin sahihin zaɓe shi ne ginshiƙin samar da shugabanci bisa ƙa’ida, ƙarfafa hukumomin gwamnati da kuma samar da yanayin da zai ba da damar samun ci gaba mai ɗorewa.
Tsohon kwamishinan zaɓen ya ce Nijeriya tana da albarkatun mutane da na ƙasa da za su iya mayar da ita ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki a duniya, sai dai tsarin zaɓen shugabanni ya gaza kare muradun ’yan ƙasar.
Ya buƙaci gwamnatin Trump da ta haɗa matakan diflomasiyya na rigakafi, sa ido kan zaɓe mai zaman kansa da kuma ɗaukar matakan hukunta waɗanda aka tabbatar da hannu cikin karya dokokin zaɓe.
A cikin shawarwarin da ya gabatar, Igini ya nemi gwamnatin Amurka da ta aika da wata tawaga mai manyan jami’ai domin ganawa da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ’yan takarar shugaban ƙasa da na gwamnonin jihohi, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), jam’iyyun siyasa da sauran hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce ya kamata tawagar ta bayyana wa gwamnatin Nijeriya matsayin Amurka na ganin an gudanar da sahihin zaɓe, gasa ta siyasa cikin lumana da kuma mutunta haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Igini ya kuma yi kira da a kakaba takunkumi kan jami’an zaɓe da aka samu da hannu wajen yin maguɗin sakamakon zaɓe da gangan, sauya bayanan zaɓe da kuma aikata wasu manyan laifukan da suka shafi zaɓe, idan akwai sahihiyar hujjar da ta tabbatar da hakan.
Ya ambaci shugaban INEC, kwamishinonin hukumar na ƙasa, kwamishinonin zaɓe na jihohi da kuma jami’an wucin gadi da ake ɗauka daga hukumomin tarayya da jami’o’i, inda ya ba da shawarar hana waɗanda aka samu da laifi shiga Amurka, tare da kakaba musu takunkumin kuɗi da ƙwace kadarorinsu idan doka ta ba da damar yin hakan.
Dangane da ɓangaren shari’a kuwa, ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta yi la’akari da ɗaukar matakan da suka dace kan jami’an shari’a da aka samu da hannu wajen cin hanci da rashawa da gangan ko wasu laifukan da ka iya kawo cikas ga adalcin zaɓe.
Sai dai ya jaddada cewa ’yancin kai na bangaren shari’a yana da matuƙar muhimmanci ga dimokuraɗiyya, amma bai kamata a yi amfani da shi a matsayin mafaka ga cin hanci da rashawa ko lalata adalcin zaɓe ba.
Tsohon kwamishinan ya kuma yi kira da a ɗora wa jami’an tsaro alhakin duk wani amfani da hukumomin tsaro wajen nuna goyon bayan siyasa a lokacin zaɓe.
Ya ce rundunar ’yan sanda, Hukumar DSS, sojoji da sauran hukumomin tsaro suna da alhakin kare ’yan ƙasa da tabbatar da bin doka ba tare da nuna son kai ba, maimakon yi wa muradun ’yan siyasa hidima.
A cewarsa, ya kamata manyan jami’an tsaro da kwamandojin da aka tabbatar da hannu wajen tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a, tashin hankalin zaɓe, danne ’yan adawa ba bisa ƙa’ida ba ko yin maguɗin sakamakon zaɓe su fuskanci hukunci, ciki har da hana su shiga Amurka da sauran takunkumai.
Igini ya ƙara ba da shawarar cewa Amurka ta tallafa wa ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe na cikin gida da na ƙasashen waje masu sahihanci, domin lura da yadda za a gudanar da zaɓen shekarar 2027 kafin lokacin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan kammala shi.
Ya ce ya kamata a mayar da hankali musamman kan tsoratar da masu zaɓe, yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son kai ba, fitar da sakamakon zaɓe na kowace rumfa, tattara sakamako cikin gaskiya da kuma warware rigingimun zaɓe.
Da yake bayyana dalilin da ya sa wannan manufa za ta amfani Amurka, Igini ya ce sahihin zaɓe da shugabanci na gari a Nijeriya za su iya rage yawan mutanen da ke ƙaura zuwa ƙasashen waje, ta hanyar samar da ingantattun damarmakin tattalin arziki a cikin gida.
Ya ce ingantaccen shugabanci zai ƙarfafa ’yan Nijeriya su zauna a ƙasarsu domin bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa, tare da jawo hankalin ’yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje su dawo gida.
Ya kuma bayyana cewa wannan manufa za ta kare dukiyar Amurka daga amfani da ita wajen tallafa wa gwamnatocin da ba su samu halaccin amincewar al’ummarsu ba, tare da ƙarfafa Nijeriya wajen haɗin gwiwa da Amurka domin yaƙi da ta’addanci, manyan laifuka da ake aikatawa cikin tsari, rashin tsaro a yankin da kuma tasirin ƙasashen da ke adawa da muradun Amurka a Afirka.
