Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Babbar Sakatariyar Zartarwa ta Asusun Tallafawa Lafiya na Jihar Kano (KHETFUND), Dakta Fatima Usman Zahararddin, ta jagoranci shirin tallafa wa mata da kuɗi, shinkafa da atamfa a ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.
Mata 1,000 ne suka amfana da shirin, inda kowacce ta samu naira 10,000, buhun shinkafa da kuma atamfa domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da inganta walwalarsu.
Da take jawabi a wajen rabon kayan tallafin, Dakta Zahararddin ta bayyana shirin a matsayin wata alama ta shugabanci mai tausayi da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke nunawa, tare da tabbatar da aniyarsa ta tallafa wa mata, zawarawa, marayu da sauran marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Ta kuma buƙaci masu riƙe da muƙaman gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan ƙuduri na tallafa wa al’umma da inganta rayuwarsu.
A nasa jawabin, Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai Rago, ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin abin koyi mai ma’ana.
Ya kuma yaba wa babbar sakatariyar bisa kawo shirin ƙarfafa mata zuwa ƙaramar hukumar tasa.
Shi ma ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Shu’aibu Rabiu Na Gwaggo, ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.
Ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyarsu da su yi koyi da irin wannan aikin alheri.
A nata jawabin, Shugabar Mata ta jam’iyyar APC, Hajiya Fatima Dala, ta bayyana farin cikinta da shirin, tare da jaddada muhimmancin rawar da mata ke takawa wajen ci gaban al’umma.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daga mazabu 15 na ƙaramar hukumar, da kuma ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar yankin, Hon. Yusuf Hussaini Datti.
An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Hafsat Ganduje da ke Dawakin Kudu.
