Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin ɓanguard Media Limited, mawallafin jaridar ɓanguard, ya shiga jimamin rasuwar editan jaridar mai kula da kafafen intanet, Olufemi Finayon Ajasa, wanda ya rasu yana da shekaru 44.
Rahotanni sun ce Ajasa ya rasu ne a ranar Lahadi, 15 ga Nuwamban 2026, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH), bayan gajeriyar rashin lafiya.
Editan jaridar ɓanguard, Eze Anaba, ne ya sanar da rasuwar marigayin cikin wata sanarwa, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga kamfanin da kuma aikin jarida.
Anaba ya ce marigayin ya kasance jajirtaccen ma’aikaci a cikin iyalan ɓanguard, wanda gudunmawarsa ta taimaka wajen ƙarfafa ayyukan jaridar na kafafen intanet da bunƙasa aikin jarida ta yanar gizo.
An haifi Ajasa ne a gidan Ajasa da ke Ajido, ƙaramar Hukumar Badagry a Jihar Legas. Ya karanci Sadarwa, inda ya ƙware a fannin aikin jarida, a Jami’ar Jihar Legas tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009, inda ya samu digirin farko na B.Sc.
A shekarar 2015, ya ƙara bunƙasa ƙwarewarsa ta hanyar samun takardar shaidar Adɓanced Writing and Reporting Skills daga Makarantar Media and Communication ta Jami’ar Pan-Atlantic.
Ajasa ya fara aikin jarida ne a watan Fabrairun 2012 a matsayin mai ɗaukar hotunan labarai a jaridar National Mirror, inda ya yi aiki har zuwa Nuwamban 2013.
A watan Disamban 2013 ya shiga jaridar ɓanguard a matsayin mai kawo labarai da samar da abubuwan da ake wallafawa a kafafen intanet, inda ya ci gaba da aiki har zuwa Satumban 2016.
Daga bisani, ya koma gidan yanar gizon TheNewsGuru.com, inda ya yi aiki daga shekarar 2016 zuwa 2021. Da farko ya kasance editan kafafen intanet, kafin daga bisani ya zama jagoran tawaga da shugaban ayyukan dijital.
A watan Disamban 2021, ya shiga kamfanin Pulse a matsayin manajan kula da ingancin aikin edita, kafin ya koma ɓanguard a watan Yunin 2022 a matsayin editan kafafen intanet, mukamin da ya riƙe har zuwa rasuwarsa.
Komawarsa ɓanguard ta nuna ci gaba da alaƙar aikinsa da jaridar, wadda ta fara tun farkon rayuwarsa ta aikin jarida.
ɓanguard ta sanar da shirye-shiryen jana’iza
Shugabannin ɓanguard Media Limited sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan marigayin, abokansa, abokan aikinsa da sauran waɗanda rasuwarsa ta shafa, tare da addu’ar Allah Ya ba su ƙarfin jure wannan rashi.
Jaridar ta ce za a gudanar da taron addu’a da zaman makoki (Serɓice of Songs and Wake-Keep) domin tunawa da marigayin a ranar Alhamis, 19 ga Nuwamban 2026, da ƙarfe 5:00 na yamma, a lamba 14, Sylvia Crescent, Anthony ɓillage, Legas.
Iyalan marigayin za su sanar da sauran shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba.
