Noman rani: Shettima ya sanar da shirin samar da buhunan taki miliyan uku domin raba wa manoma

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a masana’antar takin zamani da su gaggauta shirye-shiryen samar da buhunan takin zamani sama da miliyan uku domin rabawa manoma a faɗin Nijeriya gabanin fara noman rani.

Umarnin ya biyo bayan amincewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar ƙarƙashin shirin Sabunta Fata na Fannin Noma, wanda aka tsara domin rage farashin takin zamani, bunƙasa noman abinci da farfaɗo da masana’antun sarrafa takin zamani a Nijeriya.

Shettima ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a ɓangaren takin zamani.

A yayin taron, ƙungiyar Masu Samarwa da Rarraba Takin Zamani ta Nijeriya (FEPSAN) ta bayyana cewa akwai isassun kayan haɗin da za su iya samar da buhunan takin NPK kusan miliyan uku cikin makonni masu zuwa.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma umarci Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da ya tantance tare da bibiyar adadin takin da masu ruwa da tsaki suka bayyana cewa suna da shi, domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen rabawa.

Ya kuma buƙaci ofishin da ya tabbatar da cewa ba a ware manoman jihohin da ke fama da matsalar tsaro daga shirin ba, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke da wahalar isa.

Shettima ya ce farfaɗo da masana’antar takin zamani zai taimaka wajen bunƙasa noma, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummomin karkara.

Ya nuna damuwa kan yadda yawancin masana’antun haɗa takin zamani ke aiki ƙasa da ƙarfin da ake sa ran za su iya yi, duk da yadda buƙatar takin mai sauƙin farashi ke ƙara ƙaruwa.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu na son farfaɗo da waɗannan masana’antu domin su koma aiki yadda ya kamata, tare da dawo da ma’aikata, masu safarar kayayyaki da dillalan kayan amfanin gona bakin aiki.

Ya jaddada cewa manoma ne za su fi amfana da shirin, inda gwamnati za ta sayi takin da kamfanonin cikin gida suka samar, sannan ta sayar wa manoma kan farashi mai sauƙi.

Tun da farko, Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Abubakar Bagudu, ya ce manufar shirin ita ce rage kuɗin sayen kayan noma tare da ƙarfafa samar da su a cikin gida.

Ya bayyana cewa an gano tan 496,000 na takin zamani da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da shi, yana mai cewa wannan adadi zai zama kyakkyawan matakin farko wajen aiwatar da shirin.

Ya kuma ce gwamnati za ta nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗe daga shirye-shiryen da ake da su domin ci gaba da tallafin bayan lokacin da shugaban ƙasa ya tsara.

A nasa jawabin, Shugaban FEPSAN, Abubakar Kassim, ya yaba wa Tinubu bisa yadda ya sa baki kai tsaye wajen farfaɗo da masana’antar takin zamani.

Kashim ya ce mambobin ƙungiyar sun tabbatar da cewa akwai kayan haɗin da za su iya samar da tan 148,000 na takin NPK 20-10-10 cikin makonni masu zuwa, wanda zai kai kusan buhu miliyan uku.

Ya ƙara da cewa mambobin ƙungiyar na da tan 29,000 na takin da aka riga aka sarrafa, wanda gwamnati za ta iya saya domin fara rabawa nan take.

Ya ce masana’antar na da ƙarfin samar da takin zamani har buhu miliyan 3.5 a cikin lokacin da aka tsara, saboda akwai masana’antun sarrafa takin da wuraren ajiya a sassa daban-daban na ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply