INEC ta faɗi abin da ya sa Mark da Aregbesola ke cikin kundin ADC yayin da tsagin su Nafi’u Bala ya yi bore

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zamanta ta Ƙasa INEC, ta ce matsayarta na rikicin jagorancin jam’iyyar ADC ya ta’allaƙa ne da sakamakon ɗaukaka ƙara da aka shigar a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara akan hukuncin da ya soke jagorancin su tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark.

Tsagin su Nafi’u Bala Gombe na jam’iyyar, ya buƙaci hukumar da ta yi biyayya ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya wajen amince wa shugabancinsu tare da cire sunayen Mark da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola daga cikin kundin bayanan ADC.

Kwamishinan Ƙasa na INEC, Mohammed Haruna, ya bayyana matsayar jam’iyyar ne a ranar Laraba, inda ya ce an gabatar wa hukumar jawabin ɗaukaka ƙarar hukuncin don haka za ta jira ta ga wane hukunci za yi a kai gabanin duba irin matakin da za ta ɗauka.

Saidai, lauyan da ke kare ɓangaren su Nafi’u Gombe, wanda ƙorafinsa ya janyo hukuncin soke tsagin su Mark, ya ce akwai buƙatar INEC ta yi biyayya ga umarnin da kotu ta bayar a madadin wani sabon jira daga hukumar.

Ɗaya daga cikin lauyoyin Nafi’u Gombe, Haruna Musa SAN, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa INEC zuwa yanzu ba ta bayar da amsa ba kan wasiƙar da shugaban tsagin ya rubuta ba, wadda a ciki ya nemi hukumar ta aiwatar da umarnin kotu.

Tuni dai kwamitin amintattun ADC tsagin su Gombe, ya kirayi INEC da ta gaggauta aiwatar da hukuncin INEC ma ranar 5 ga Nuwamba, 2026 kan rikicin jagorancin jam’iyyar, wanda ya kuma buƙaci a cire sunayen su Mark da Aregbesola daga kundin jagororin jam’iyyar.

By Babaji

Leave a Reply