An yi hasashen al’ummar Musulmi za su kere Kiristanci a yawan jama’a nan da 2035

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ana hasashen addinin Islama zai iya kere Kiristanci a yawan jama’a zuwa nan da shekarar 2035, inda ake tsammanin a samu ƙarin hauhawar haihuwa acikin matan Musulmi, a cewar wani bincike da cibiyar Pew Research Center ta yi.

An ƙiyasta adadin al’ummar Musulmi ya kai biliyan 2.57 nan da 2035, wanda zai ɗara yawan Kiristanci mai mutane biliyan 2.5 a lokacin, wanda zai taimaka wajen samu gagarumin sauyi a duniya ganin cewa Kiristanci ya zama addini mafi yawan jama’a a tsawon ɗaruruwan shekaru.

Binciken ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2070, adadin Musulmi a duniya zai iya haura mutum biliyan 3.6, wanda zai wakilci kusan kashi 36 cikin 100 na al’ummar duniya.

Rahoton ya bayyana cewa yawan haihuwa a iyalan Musulmi, da kuma kasancewar mafi yawan Musulmi matasa, na daga cikin manyan dalilan da ke haifar da wannan ƙaruwa.

Haka kuma, binciken ya yi hasashen cewa ƙasar Pakistan ce za ta kasance ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan Musulmi a duniya.

By Babaji

Leave a Reply