Baffa Babba Dan Agundi mutum ne mai kishin al’umma da son bunƙasa ci gabansu — SMK

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Alhaji Sani Muhammad Kurmawa, ɗaya daga cikin waɗanda suka bayar da gudummawa a shirin horas da matasa na ƙungiyar Gyara Kayanka da Dakta Baffa Babba Dan’agundi ya ɗauki nauyin gudanarwa, ya bayyana cewa Allah ya azurta al’ummar ɗan’agundi da jajirtaccen mutum mai kishin unguwarsu, wato Dakta Baffa Babba ɗan’agundi.

Ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da shirin horas da matasa 156, wanda Hon. Baffa Babba Dan’agundi ya ɗauki nauyin ba su horo kan sana’o’i tare da samar musu da jari bayan kammala horon, domin su zama masu dogaro da kansu a cikin al’umma.

Ya ce tun a baya, Dakta Baffa na gudanar da irin waɗannan tallafe-tallafe ga matasa a ɓoye, ba tare da bayyana wa jama’a ba, har daga baya aka san da ayyukansa, inda ya fito fili. Ya ƙara da cewa kusan kullum aikin Dakta Baffa kenan, wato tallafa wa al’umma.

Ya ce ana tallafa wa wasu da kuɗin makaranta, wasu kuma saboda rashin lafiya, wasu don batun aure, wasu don gyaran gida, yayin da wasu ake taimaka musu da abincin da za su ci tare da iyalansu. Ya bayyana cewa irin waɗannan tallafe-tallafen ba za su ƙirgu ba.

Alhaji Sani Muhammad Kurmawa ya ce a halin yanzu, idan aka tashi daga unguwar ƙofar ɗan’agundi har zuwa ƙofar Kudu, aka bi ta Asibitin Asiya Bayero, aka shiga har ƙofar Naisa, sannan aka dawo har ƙofar Nasarawa, babu wanda yake gudanar da irin taimakon da Baffa Babba ɗan’agundi yake yi. Saboda haka, sun yi farin ciki da jin daɗi tare da gode wa Allah da ya azurta su da shi.

Ya bayyana cewa abin da ya ja hankalinsa har ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu (N2,000,000), shi ne domin ya ƙara masa ƙwarin gwiwa. Ya ce kamar yadda shi ya zo ya bayar da gudummawa mai yawa, haka kowa zai iya bayar da abin da yake da iko, domin shi ne abin da ya kamata. Ya ƙara da cewa ko wanda ya zo ya bayar da ƙwandala, naira 300 ko 1,000, shi ma ya bayar da gudummawa, abin da Allah yake kallo shi ne an yi ne domin Shi.

Ya ce matasan da za a koya wa sana’o’i, a tallafa musu da jari, sannan a tarbiyantar da su, ƙannensu ne, wasu kuma ’ya’yansu ne. Idan sun gyaru, to unguwar ɗan’agundi ma ta gyaru.

Ya ce abin jin daɗi ma shi ne yadda jami’an NDLEA da Civil Defence suka bayar da kyakkyawar shaida kan matasan ɗan’agundi, inda tun daga fara aikin ƙofa har zuwa kammalawarsa, ba su ga wani abu na rashin tarbiyya a wajen matasan ba. Ya ce wannan babban abin alfahari ne a gare su, musamman idan aka yi la’akari da irin gudummawar da ake bayarwa.

Alhaji Sani Muhammad Kurmawa ya yi kira ga matasan da za a horas da su sana’o’i tare da ba su jari da cewa idan suka fara kowace irin sana’a, su shiga cikinta da ƙwarin gwiwa, su dage, su riƙe gaskiya da amana. Ya ce wannan shi ne matakin da za su ɗauka domin samun bunƙasa.

Ya kuma shawarce su da su yi haƙuri da jajircewa, yana mai cewa idan suka riƙe waɗannan ƙa’idoji, za su samu rufin asiri a rayuwarsu.

By ukarofi

Leave a Reply