
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun tarwatsa turaken lantarki guda biyu da ke haɗa tashar lantarki ta madatsar ruwan Kainji da Jebba a Jihar Neja.
Al’amarin ya auku ne a ranar 17 ga Nuwamba da misalin ƙarfe 2 na rana a tsakanin ƙauyen Kanti a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ƙauyen Kanya a Ƙaramar Hukumar Mokwa na jihar. A cewar wata majiyar soji da ta tabbatar wa ‘yan jarida, an yi zargin cewa an shirya lalata layin lantarki ne da harin tashar wuta ra “Kainji Dam”.
Waɗannan fashe-fahse sun haifar da firgici acikin al’ummar yankin yayin damuwa kan hare-hare akan kayayyaki lantarkin ƙasa.
Majiyar ta ce, babu asarar rai a sanadiyyar aukuwar lamarin kuma jami’an tsaro suna sanya ido a wajen domin bayar da kariya ga yiwuwar ƙarin wasu hare-haren ‘yan ta’adda. Wannan al’amari ya faru ne a daidai lokacin da ake samun ayyuka lalata kayayyakin lantarki a sassan daban-daban na Nijeriya.
A watan Nuwamba ne dai Majalisar Wakilai ta yanke shawarar binciken lalata wasu turaken wutar lantarki guda 10 acikin wata biyar a sassan jihohin Arewa uku da suka haɗa da na Kano zuwa Bauchi, Katsina da Kaduna.
