Jaruma Firdausi Yahaya ta janyo cece-kice bayan ta ci balangu akan takardar muƙaminta na tafiyar Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jarumar finafinan masana’antar Kannywood, Firdausi Yahaya ta janyo hankulan masu amfani da kafafen soshiyal mediya bayan ta fice daga tafiyar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC zuwa jam’iyya mai mulki, APC.

Rahotanni sun ce, jarumar ta bar ADC ne ƙasa da wata guda da ta ziyarci Atiku a gidansa kuma ya ba ta muƙamin zama ɗaya daga cikin masu masa yaƙin neman zaɓe a shiyyar Arewa maso Yamma.

Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da jaridar The Nation ta wallafa, ya nuna yadda Firdausi Yahaya ta yi amfani da takardar bayar da muƙamin da ‘yan tafiyar Atiku suka ba ta wajen ƙunshe tsire a ciki da lanƙwamewa. Bidiyon ya bayyana ne biyo bayan rahotannin da ke cewa jarumar ta fice daga ADC ta koma APC a bayan makonni kaɗan da suka wuce da ta gabatar da kanta a matsayin ‘yar tafiyar Atiku kuma ta nuna takardar shaidar ba ta matsayi a cikin tafiyar.

A cewar rahotanni, a takardar mai kwanan wata 30 ga Oktoba, 2026, an ayyana ta a matsayin Daraktar Mata da Damawa da Al’umma a ƙarƙashin ofishin Mai Taimaka wa Atiku na Musamman kan Tattara Matasa a Arewa maso Yamma. Matakin jarumar na yanzu ya haifar da cece-kuce, inda wasu masu amfani da kafafen soshiyal mediya suke bayyana mamakinsu a kai, yayin da wasu suka mayar da hankali kan yadda ta yi wa takardar bada muƙamin bayan sauya sheƙar tata.

Firdausi Yahaya, wadda aka sani da Zainab Labarina, jarumar Kannywood ce da aka san ta da fitowa a finafinan Hausa da shirye-shiryen talabijin. Ta samu shahara ne a lokacin da ta fito a matsayin matsayin Zainab matar Al’ameen a fitaccen fim ɗin nan mai suna Labarina.

Haka kuma, ta fito a finafinai kamar su Garwashi, Jamilun Jidda da Allurar Cikin Ruwa da dai sauransu. Sannan, an ce jarumar ta shiga harkar fim ne ta hannun wani ɗan uwa da ya gabatar da ita ga fitaccen daraktan nan mai suna Aminu Saira, wanda ya zama ɗaya daga cikin jiga-jiganta na farko a masana’antar fim.

By Babaji

Leave a Reply