Matsin rayuwa da ake ciki zai iya jefa APC cikin matsala a Arewa – Sanata Kawu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Kawu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar ƙalubale wajen samun goyon bayan al’ummar Arewa sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a ƙasar.

Kawu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ, inda ya ce tsare-tsaren sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu sun jefa jam’iyyar cikin ƙalubalen shawo kan masu zaɓe, musamman a Arewacin Nijeriya.

Ya ce dole ne shugabannin APC su tausaya wa al’umma, su saurari kokensu tare da bayyana irin amfanin da manufofin gwamnati za su samar, maimakon dogaro da gangamin siyasa kawai.

“Mutane ba sa farin ciki saboda halin wahalar da suke ciki,” in ji shi.

Sanatan ya ce jam’iyyar na buƙatar komawa cikin al’umma domin tattaunawa kai tsaye da masu zaɓe, sauraron matsalolinsu da kuma bayyana musu matakan da gwamnati ke ɗauka.

Ya kuma bayyana cewa APC na da ƙalubalen dawo da amincewar al’ummar Arewa gabanin zaɓen 2027, amma yana ganin za a iya sauya yanayin siyasar cikin kwanaki 60 idan jam’iyyar ta ɗauki matakan da suka dace.

Kawu ya ƙara da cewa APC za ta yi aiki wajen samun goyon bayan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, duk da ikirarin ’yan adawa na cewa za su samu nasara a yankunan.

Sanatan ya kuma amince cewa matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ke damun al’umma, inda ya buƙaci jam’iyyar ta riƙa bayyana ayyukan gwamnati a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa.

A wani ɓangare na hirar, Kawu ya kare matakin komawarsa APC a shekarar 2025, bayan ya fice daga NNPP, inda ya ce ya ɗauki matakin ne domin samun damar amfani da matsayinsa a Majalisar Dattawa wajen samar da ayyukan ci gaba ga al’ummar mazabarsa.

Ya jaddada cewa komawarsa APC ba yana nufin ya daina sukar shugabancin jam’iyyar ba, yana mai cewa har yanzu yana jan hankalin shugabanninta kan abubuwan da yake ganin ya kamata a gyara.

By ukarofi

Leave a Reply