Wata ‘yar yawon buɗe ido ta zargi Sarkin Daura da cin zarafinta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata mata mai suna Beduinqa wadda ta ce ta kammala rangadin kwanaki 30 a sassa daban-daban na Najeriya, ta zargi Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, da cin zarafinta ta hanyar taɓa jikinta ba tare da izininta ba.

Matar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce lamarin ya faru ne yayin da ta kai ziyara fadar Sarkin Daura a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026.

A cewarta, an kai ta wani ɗaki a cikin fadar, inda suka zauna suna tattaunawa, amma daga bisani Sarkin ya fara wasa da hannunta, sannan ya rungume ta tare da sumbatar kumatunta.

Ta ce abin da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda daga bisani Sarkin ya kama nonuwanta, lamarin da ya sa ta nuna rashin amincewarta tare da bayyana masa cewa ba ta yarda ya taɓa jikinta ba.

Ta ƙara da cewa duk da nuna rashin yardar ta, Sarkin ya ci gaba da dariya kamar babu wani abin da ya faru.

Matar ta ce ba ta taɓa fuskantar irin wannan cin zarafi ba a tsawon lokacin da ta yi tana zagayawa a sassan Najeriya, ciki har da wuraren da jama’a ke taruwa.

Ta bayyana cewa lamarin ya jefa ta cikin damuwa da takaici, inda ta ce har yanzu tana yawan tunawa da abin da ya faru.

Ta ce ta jira har sai da ta bar Najeriya kafin ta bayyana lamarin a bainar jama’a, tana mai zargin cewa mai yiwuwa ba ita ce mace ta farko da ta fuskanci irin wannan yanayi ba.

Ta kuma bayyana cewa tana sanye da tabarau masu ɗaukar bidiyo na kamfanin Meta a lokacin ziyarar, kuma ta kunna su lokacin da lamarin ya faru, abin da ta ce ya ba ta damar samun hotunan abin da ya faru.

Da yake maida martani sarkin labarai na Sarkin Daura Alhaji Ibrahim Murtala Daura a wata hira da gidan rediyo na Alfijir yace masarautar na sane da bidiyon da ya karaɗe kafafen zumunta.

Yace masarautar za ta tantance sahihancinsa domin ganin ba a yi amfani da wata fasaha ko ƙirƙira wajen sauya ta ba.

Sarkin labarai yace za su fitar da sanarwar a hukumance bayan kammala binciken.

By ukarofi

Leave a Reply