Gwamna Lawal ya ƙaddamar da yaƙin neman wa’adi na biyu a Talata Mafara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, a ranar Litinin ya ƙaddamar da yaƙin neman wa’adi na biyu a garin Talata Mafara.

Ƙaddamarwar, wacce ta nuna fara yaƙin neman sake zaɓen Gwamnan a hukumance gabanin babban zaɓen shekarar 2027, ta mayar da Talata Mafara wuri mai cike da nishadi da launuka daban-daban yayin da magoya baya suka fito domin tarbar Gwamnan da tawagarsa.

Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka halarta, Gwamna Lawal ya jaddada shirin gwamnatinsa na ceto Jihar Zamfara da kuma ƙarfafa nasarorin da aka samu a wa’adinsa na farko.

Ya ce gwamnatinsa ta karɓi mulki a lokacin da Zamfara ke fama da matsalar rashin tsaro mai tsanani, lalacewar ababen more rayuwa, rashin biyan albashi, da durƙushewar tattalin arziki, amma ta yi aiki tuƙuru domin dawo da fata, kwanciyar hankali da ƙwarin gwiwa ga al’umma.

A cewar Gwamnan, shirin ceto Zamfara ba wani taken baki ba ne kawai, illa wani shiri ne na aiki wanda ya riga ya fara sauya jihar.

Gwamna Lawal ya lissafa tsaro, samar da ayyukan yi, ci gaban ɗan Adam da ci gaban ababen more rayuwa a matsayin manyan abubuwan da za su fi ba shi fifiko a wa’adinsa na biyu.

A kan tsaro, ya ce gwamnatinsa ta zuba jari mai yawa wajen tallafawa hukumomin tsaro, ƙarfafa jami’an tsaron al’umma, da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin dawo da zaman lafiya ga al’ummomin da ke fama da matsala, kuma za ta ƙara yin hakan a wa’adinsa na biyu domin tabbatar da cewa manoma sun koma gonakinsu kuma ‘yan kasuwa na tafiya cikin ‘yanci ba tare da tsoro ba.

A kan samar da ayyukan yi, Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta faɗada shirye-shiryen ƙarfafa al’umma, tallafawa ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, da samar da ƙarin damammaki ga matasa da mata domin su dogara da kansu.

A kan ci gaban ɗan Adam, ya yi alƙawarin ci gaba da zuba jari a ɓangaren ilimi, lafiya, da koyon sana’o’i, yana mai cewa babu wata jiha da za ta ci gaba ba tare da al’umma masu ilimi da lafiya ba.

A kan ci gaban ababen more rayuwa, Gwamna Lawal ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da gagarumin aikin gina da gyaran hanyoyi, makarantu, asibitoci, ruwan sha, da sauran muhimman ababen more rayuwa a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

“Tsaro, samar da ayyukan yi, ci gaban ɗan Adam da ci gaban ababen more rayuwa za su ci gaba da zama manyan abubuwan da muka fi ba da fifiko. Mun fara aikin ceto Zamfara, kuma ba za mu tsaya ba har sai Zamfara ta zama jihar zaman lafiya, arziki da alfahari ga kowa da kowa,” in ji Gwamna Lawal.

Gwamna Lawal ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su ƙara ba shi goyon baya da kuma wani wa’adi domin kammala aikin alheri da ya fara.

Ya roƙi al’ummar Talata Mafara da Zamfara baki ɗaya da su tsaya tare da shi, su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, su kuma ki amincewa da siyasar rarrabuwa, tashin hankali da alƙawuran ƙarya.

Ya ce gwamnatinsa gwamnati ce ta dukkan ‘yan Zamfara, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa, addini ko ƙabila ba, kuma ya yi kira ga dukkan ‘yan ƙasa da su haɗa hannu wajen gina sabuwar Zamfara.

“Ina rokonku da ku kara ba ni goyon bayanku. Ku ba ni wa’adin ku domin in kammala abin da muka fara. Tare, za mu ceto Zamfara gaba daya,” ya ce cikin tafi da murna.

Tun da farko, shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Talata Mafara da faɗin jihar, ƙungiyoyin mata, ƙungiyoyin matasa, da shugabannin al’umma sun yi ta tofa albarkacin bakinsu suna bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Gwamnan, suna bayyana gwamnatinsa a matsayin gwamnati mafi kyau da Zamfara ta samu a cikin ‘yan shekarun nan.

Sun ce Gwamna Lawal ya dawo da biyan albashi akai-akai, ya inganta ɓangaren ilimi, ya farfaɗo da ɓangaren lafiya, kuma ya nuna jajircewa ta musamman wajen magance rashin tsaro.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki na APC, mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha, mambobin Majalisar Dokokin Jiha, Shugabannin Ƙananan Hukumomi, da dubban magoya bayan jam’iyya.

Blueprint ta ruwaito cewa ana sa ran tawagar yaƙin neman zaɓe ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar dinta, Alh. Salihu Maibuhu Gummi, za ta wuce zuwa sauran Ƙananan Hukumomi a cikin kwanaki masu zuwa yayin da Gwamna Lawal ke ƙara zafafa yaƙin neman sake zaɓensa a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply