Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ko na yi niyyar dasa aya kan labarun ‘yan ta’adda da asalin fitinar jihar Filato sai na ga wani ya yi wuf ya na ƙara harbin iskar ƙarshe na murɗe wuyan dalilan kashe-kashen zuwa wai makiyaya ne ke addabar masu iƙirarin ‘yan kasa don haka su ke kare kansu. Abun ƙarin godiya ga Allah su Jasawa da mazauna sauran sassan jihar ta Filato na adane gam-gam da bayanan tsantsar gaskiyar abubuwan da su ka auku kama daga 2001.
A ranar 19 ga watan Janairu na 2010 ‘yan ta’adda daga Birom sun yi cincirindo su ka zagaye garin Kuru Karama da ke yankin Jos ta Kudu kilomita 30 a kudancin Jos su ka sheƙe Hausawa da ma wasu Fulani mazauna garin.
‘Yan ta’addan ɗauke da gatura, gariyo da bindiga sun yi dirar mikiya kan Hausawa maza da mata yara da ma jarirai su ka kashe kimanin mutum 170 da a ka iya ganowa. Tsarin kisan ya haɗa da bankawa Hausawa Musulmi wuta a cikin gidajensu da ma babban masallacin Kuru Karama inda su ka ƙurewa wasu gudu su ka zabga mu su gayawa jini na wuce! Wallahi wasu mutanen sun kone ta yadda ko gane su ba za a iya yi ba sai dai in an kasa gano wani sai a yi kintace a ce ya na daga waɗanda a ka mayar toka.
‘Yan ta’addan waɗanda a ka yi amanna duka mabiya addinin Kirista ne da su ka ki aiki da tausayi na Baibul, sun jefa gawawwakin mutane cikin rijiyoyi da ma salga don tsananin wulaƙanci.
Baya ga kashe duk wanda su ka samu, ‘yan ta’addan sun ruguje gidaje da masallatai da shaguna. Ba abun da ke zuciyarsu a lokacin illa su shafe mutanen daga doron kasa don tunanin su kadai su zauna a jihar su yi rawar banjo.
Mutanen nan da ‘yan ta’adda Beromawa su ka sheke ba su tura mu su shanu gonakin dawa ko sun kashe mu su aladu ba, a a laifinsu shi ne Hausawa ne kuma musulmi.
Illar ‘yan ta’addan Beromawa sun ɗauka za su sheƙe dukkan Hausawa daga jihar Filato sai su kuma su zauna lami lafiya ba mai ce mu su cas ba as!!.
Duk mai alaƙanta fitinar Filato da wai Fulani makiyaya ne ke tsokanar manoma ya zama tantirin mai murɗe wuyan gaskiya. Hatta makiyayan na fadar yadda Beromawa sam ba sa so su yi kiwo a jihar duk da a tsawon shekaru sun zauna tare amma sannu a hankali sai wani ya sheke wani don samun damar kashe shanu da cin ganimar nama na Bello Badun.
An yi taruka da kwamitocin neman zaman lafiya amma wanda ya ji dadin naman saniya na bulus ko a ke haɗa kai a kai kara gun jami’an tsaro abun da bai fi kudin akuya ba ya juye shanu goma; sai ya rikito fitina don kar a samu salama.
Shin me ya faru a Yelwa, Gangaren Riyom ‘yan dankali, cinnawa kasuwar Terminus wuta, Dogo Nahawa, ‘yan kasuwa a hanyar Pankshin da sauran labaru masu ban takaici?
Yadda ‘yan ta’adda daga Birom a 2011 su ka zagaye jasawa a masallacin idi su ka kashe su da kona kimanin motoci 200. Ko na nemi dasa aya hakanan kan asalin fitinar Filato ta kiyayyar bambancin addini da wasu ke murɗewa zuwa wai tura shanu gonar dawa, sai na ga da sauran ruwan alƙalami ko tawada a kurtuna.
Wallahi ni kai na na shigo Jos zan wuce da almuru a ranar 29 08 2011 da matasa Beromawa su ka yi cincirindo su ka datse tituna da yi wa musulmi masu halartar sallar idin ƙaramar sallah a RUKUBA ROAD kofar rago su ka sheƙe na sheƙewa su ka ƙone kimanin motoci 200 kuma cikin wasu daga motocin har da yara ƙanana!!!
Da farko Beromawa sun yi ta majajjawa da ruwan duwatsu da kibau inda daga bisani gariyo da barandami har da albarusai su ka biyo baya. Hakan ya tuno min da labarin da Malam Aminu Kano ya rubuta a TAFIYA MABUDIN ILIMI in na nakalto daidai na karar wucewar makamai GUN-GUN TSU GUN-GUN TSU.
Rahoto ya tabbatar da liman bai samu isowa ba don tare hanya da a ka yi ga mutane kar su isa can RUKUBA ROAD su fada tarkon ‘yan ta’addan na Beromawa. Nan dai Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya jagoranci sallar inda masu jifa da harbi su ka takarkare don gamawa da dukkan Jasawa da su ka halarci sallar bayan kammala azumin Ramadana.
An samu tsaiko na kimanin sa’a 5 kafin Sheikh ya yi umurnin a yi yunƙurin ficewa daga bigiren. Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan jingir da sauran manyan malamai na wajen. Maganar shiga mota ma ba ta taso ba don Beromawa sun bankawa motocin wuta duk da ba saniya ko daya a motocin.
Cikin ikon Allah Sheikh Sani Yahaya da wasu jama’a su ka isa gida kuma an ruwaito Sheikh din na shaidawa manema labaru yadda duwatsu da albarusai su ka yi ta keta inda ya ke amma Allah ya sa da sauran shan ruwa. Sheikh ya ce a shekaru 30 su na sallah a masallacin amma ba su taba fuskantar farmaki ba sai wannan na 2011 ya na mai kiran hukumomi su yi wa kowa adalci don samun salama.
Cikin dalilan da a ka tattara na aukawa Jasawa da Beromawa su ka yi akwai wai harin Boko Haram da kan sassan Jos da ma kan ofishin majalisar ɗinkin duniya a Abuja. Hatta shi kansa Sheikh Sani Yahaya Jingir a 2015 ya samu farmakin Boko Haram a lokacin tafsirin azumi a masallacin ‘Yantaya inda mutane da dama su ka rasa rai. Maimakon neman zaman lafiya a Jos da sassan jihar Filato, sai ‘yan ta’adda daga Beromawa su ka nemi shekar da jinin Jasawa Hausawa da Fulani da sauran masallata a filin idin.
A bayanina na farko na ce na shigo Jos a ranar na biyo ta gefen majalisar dokoki na ratso tsakiyar garin har sai da na hau Bauchi ROAD kafin na fara ganin zirga-zirga. Lamarin ya sa na fahimci akwai wani abu da ya wakana ashe kuwa da walakin goro a miya. Wallahi ni kaɗai ke tafiya a mota na zo kan marabar titin Bauchi inda a ke tsayawa a yada zango sai na ga an taru a na maida bayanin farmakin da a kai a sallar idi. Ina kan hanya sai na tada mota mu ka gangara inda kafin mu isa daidai gidajen ɗalibai jami’ar Jos a Naraguta sai mu ka tarar ‘yan ta’addan sun tare titi sun bankawa tayu wuta su na jira mu iso su ma na gayawa jini na wuce. Nan mu ka yi ribas mu ka dawo kan magamar hanya. Sai daga bisani motocin sojoji masu sulke su ka shiga gaba mu ka bi su a baya su ka raka mu har daf da gangarar nan ta zuwa Tilde.
Wallahi ba mai ƙaho a cikinmu balle saniya amma haka abokan burmin Beromawa su ka so hallaka mu.
Juyayin zubar da jinin Musulmi masu dankali a Kuru “Babba” da miyagu cikin Birom su ka yi. Kamar dai yadda ‘yan ta’adda Beromawa su ka sheƙe al’ummar Kuru Karama a 2010 su ka mayar da garin Kufayi, hakanan su ka sheke ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani da ke sayar da dankalin turawa, doya da sauran kayan lambu a Kuru “Babba”.
Duk mai bin hanyar Jos ta Kudu ko in ya gangaro daga Tahoss Riyom a shekarun baya ya san wani matsuguni a nan bakin titi mai masallaci da rijiya inda mutane kan tsaya da motocinsu don yin sallah, cin abinci da sayan dankalin turawa, doya ko sauran kayan lambu.
An wayi gari watarana ‘yan ta’adda Beromawa sun aukawa al’ummar garin su ka sheƙe su inda bincike ya nuna akwai wasu da su ka tsira sun kaura zuwa Magama Gumau a jihar Bauchi. Haƙiƙa ko daga Hawan Kibo ne ko daga kokuwar Jos ta Arewa, ba zan tuna wani bigire mai masallaci da Musulmi kan tsaya ba sai wannan waje mai albarka. Akalla akwai wasu Terawa ‘yan asalin Gombe da na san sun zauna a bigiren amma ban san ko su na raye ko ‘yan gayawa j!ni na wuce sun rutsa da su ba.
Kakaf hatta kasuwar kayan lambu ta Jonah Jang da duk masu sayar da dankali na garuruwan karamar hukumar Riyom har cikin Jos ba waje mai farin jini irin wannan matsuguni kuma don albarkacin Musulunci su ka samu ɗaukaka na tsayawa a garinsu da sayan kayansu.
Wannan bigire dai yanzu ya zama Kufayi kuma wanda bai san yadda wajen ya ke a da ba zai ɗauka kamar tsohon zama ne da a ka sauya matsuguni don akwai bishiyoyi da ke nuna mutane sun taɓa zama a wajen.
Daga bisani wata mata Ba-Biromiya kan kasa dankali a daf da wajen amma masu tsayawa na asali ba sa tsayawa a wajen don lura da hatsarin mutanen nan masu yunƙurin murɗe wuyan gaskiya.
Mutanen nan ban da sayar da dankali da danginsa ba su da shanu balle su auka gonar dawar Birom kuma Musulmi ne don haka ba za su sace aladun Birom ba don shan lagwadar aljifan baya. In ma mutanen nan Hausawa da ‘yan uwansu da a ka sheke na da wasu dabbobi ba su wuce kaji da agwagi ba.
KAMMALAWA
Shin akwai wanda ya taba binciken ko an cafke wadanda su ka yi wannan ta’addanci? Ko da wasa kar wani ya tsaya bawali ko ma ya yi alwala ya zaro sallayarsa a bigiren nan don ba alamun miyagun nan sun yi nadama.
Shin yaushe masu tare hanya a yankin jihar Filato za su tuba su shiga sahun matasan nan masu bin motar fasinja da gudu su na tallar FIYA, KARAS, ATILE da tsamiyar biri a digar jirgi ta Riyom?.
