Ana jimamin rasuwar yayan Gwamnan Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang na Jihar Filato ya shiga halin jimami sakamakon rasuwar yayansa, Arc. Morris Manasseh Mutfwang, wanda ya rasu a daren wayewar Talata bayan fama da wani rashin lafiya. Mataimakiyar gwamnan jihar, Ngo Josephine Piyo da Majalisar Harkokin Addinai ta jihar sun kai ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Rahotanni sun ce mataimakiyar ta jagoranci mambobin Majalisar Zartarwar jihar zuwa ta’aziyyar a gidan gwamnan da ke tsohon gidan gwamnatin jihar a Jos, inda ta bayyana mamacin a matsayin “mutum mai mutunci da ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar iyalansa kuma ɗan Nijeriya mai kishin da ya bai wa al’umma gagarumar gudumawa”.

A cewarta, majalisar zartarwar ta koka bisa samun labarin rasuwar, wanda ba ga iya iyalan Mutfwang aka yi shi ba, saidai rashi ne da ya shafi jihar Filato da ma ƙasa baki ɗaya, musamman duba da irin gudumawa da ya bayar don ci-gaban al’umma. Piyo ta kuma miƙa saƙon ta’aziyyarta ga gwamnan da iyalana marigayin tare da fatan ubangiji ya ba su haƙurin juriyan rashinsa.

A wata ziyarar, majalisar harkokin addinan jihar, ta jajenta wa gwamnan da iyalansa kan rashin Morris Manasseh Mutfwang. Tawagar majalisar ta ƙunshi Sarkin Alhaji (Dr.) Muhammadu Sambo Haruna a matsayin jagora, wanda ya yi jawabi a madadin shugaban majalisar, Rev. Farfesa Pandam Yamsat, inda ya bayyana rashin a matsayin babban rashi ga iyalan da kuma jihar Filato. Ya kuma yi fatan ubangiji ya ba su ikon juriyan al’amarin.

Tuni dai iyalan suka sanar da cewa za a yi jana’izar marigayin a ranar 26 ga Nuwamba, 2026, kamar yadda Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gyang Bere ya bayyana a Jos, ranar Litinin.

By Babaji

Leave a Reply