Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da duk wani taro a hukumance da tafiye-tafiyen Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, biyo bayan zargin cin zarafin wata ‘yar yawon buɗe ido ‘yar kasar waje. Gwamnatin ta kuma kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin tare da gabatar da shawarwarin matakin da ya dace.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Bala Salisu Zango, ne ya sanar da matakin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan yaɗa wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta da kuma zarge-zargen da suka shafi Sarkin da ‘yar yawon bude ido, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a. Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana damuwarsa kan zargin tare da bayar da umarnin kafa kwamitin bincike cikin gaggawa.

Gwamnatin ta ce tana ɗaukar zargin da muhimmanci, kuma za ta dogara da sakamakon binciken kwamitin wajen yanke hukunci kan matakin da ya dace. Ta kuma tabbatar da cewa za a aiwatar da shawarwarin kwamitin tare da tabbatar da adalci. Sai dai har yanzu ba a bayyana sunayen mambobin kwamitin, wa’adin binciken ko lokacin da za a gabatar da rahoton ba. Gwamnatin ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kiyaye doka, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da binciken ke gudana.

By ukarofi

Leave a Reply