
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta fara shirin kafa Hukumar Kula da Harkokin Dillancin Gidaje domin duba matakan hauhawar farashi da warware wasu matsaloli da ba sa kan ƙa’ida a fannin kadarorin jihar, yayin da ita ma Majalisar Dokokin Ƙasa take duba yiwuwar samar da hukumar ƙasa da za ta sanya ido kan lamuran gudanar da harkokin dillancin gidaje a sassan ƙasar.
Kwamishinan Ci-gaban Gine-ginen jihar, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu ne ya bayyana haka a rana Laraba yayin ganawa da ‘yan jarida jim-kaɗan bayan bayar da kariya ga kwafin kasafin ma’aikatar a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano. Ya ce, ma’aikatar ta aike wasiƙa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ke neman a samar da hukumar, inda ya ƙara da cewa buƙatar na jiran dubawar gwamnan.
Yakubu Adamu ya bayyana cewa cewa, hukumar za ta kula da lamarin gudanar da harkokin dillancin siye da bayar da hayar gidaje, da duba zargin ƙarin kuɗi mara misali daga ɓangaren dillalai da warware matsalolin da suke haddasa tsadar hayar gidaje a jihar. Haka kuma, ya ce Majalisar Dokokin Ƙasa tana duba yiwuwar samar da dokar kafa hukumar ƙasa da za ta riƙa kula da harkokin dillancin gidaje a sassan ƙasar.
A cewarsa, Majalisar Dokokin Ƙasa ta ofishin Kakakinta kuma Shugaban Kwamishinan Gine-gine da Muhalli, Abdulmumini Jibril Kofa, ta gayyaci ma’aikatar domin bayar da shawarwari akan dokar da ake shirin samarwa makonni biyu da suka gabata, yana mai cewa za a fifita ayyukan gine-gine a sassan jihar.
Daga cikin ayyukan ayyukan akwai samar da rukunin gidaje na Gwangwan Housing Estate, Gida Gida Mega City da Rural Model Cities, waɗanda aka tsara gudanarwa a ƙananan hukumomi 36 da wasu ayyuka. Sauran ayyukan sun haɗa da rukunin gidajen kwamishinoni, CDS da sashen ma’aikata na filin jiragen sama na Malam Aminu Kano International Airport da dai sauransu.
