Tinubu ya ba wa iyalan mamatan hatsarin jirgin NAF a Ondo miliyan N100 da gidaje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da gidaje masu girman ɗaki uku ga iyalan jami’an sojoji da fararen hula da suka rasu a ranar 5 ga Oktoba, 2026 a hatsarin jirgin sojojin saman Nijeriya. Haka kuma, ya amince da ware Naira miliyan 100 a matsayin ɓangare na tallafin Gwamnatin Tarayya ga iyalan mamatan.

Shugaban ya sanar da wannan kyautar ne a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026 yayin taron tunawa da su da bikin ajiye furanni don karrama mamatan su guda 25 na hatsarin jirgin NAF ATR 42. Ya ce, kyautar gidajen nuna godiya ne daga ɓangaren ƙasar akan hidimar da mamatan dakarun suka yi wa ƙasa da sauran waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin.

“A matsayin ɓangare na nuna godiyar ƙasa, na amince da ware gidaje masu girman ɗaki uku a aikin Sabunta Fata na Rukunin Gidaje a Abuja ga iyalan kowane ɗaya daga cikin jami’an sojojin da suka rasa rayukansu a hatsarin,” inji shugaban.

Shugaban ya ƙara da cewa, wannan mataki zai shafi iyalan fararen hular da suka rasu tare da sojojin a sanadiyyar aukuwar iftila’in.

By Babaji

Leave a Reply