Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
ƙungiyar Rijistirori ta Kwalejojin Ilimi ta Nijeriya (Conference of Registrars in Colleges of Education in Nigeria — CORECOEN), ƙarƙashin jagorancin Dakta Mahamud Sarki, ta gudanar da taronta na ƙasa karo na 66 a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo, a tsakiyar makon da ya gabata.
A jawabinta bayan buɗe taron, Dakta Atika Bala Maiyafe, Babbar Magatakardar Kwalejin Sa’adatu Rimi kuma shugabar babban kwamitin gudanar da taron, ta ce taron rijistirorin kwalejojin ilimi na Nijeriya da aka gudanar a kwalejin ya yi armashi, kuma babban alheri ne ga kwalejojin ilimi da al’ummar Nijeriya. Ta ce taron zai taimaka wajen bunƙasa ilimi, sabanin a baya lokacin da ba a samun irin wannan dama.
Tun da farko, babban mai masaukin baƙi kuma shugaban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kano, ya bayyana muhimmancin taron da CORECOEN ke gudanarwa duk shekara domin kawo ci gaba.
Ya ce taron na bana ya zo da sabon salo, inda ake ƙoƙarin aiwatar da shirin da zai ba ɗalibin da ya kammala karatun NCE na shekara uku damar wucewa kai tsaye zuwa digiri, ya yi ƙarin shekara biyu a kowace kwalejin ilimi da ke Nijeriya. A cewarsa, cikin shekara biyar ɗalibi zai kammala digiri tare da samun takardar shaidar NCE da ta digiri a lokaci guda.
Ya bayyana cewa wannan sabon tsari, wanda Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, ana kiransa Implementation of Dual Mandate Policy (I.O.D.M.P). Taken taron ya mayar da hankali ne kan ƙalubale da mafita, da kuma rawar da rijistirori za su taka wajen samun nasarar tsarin.
Shugaban kwalejin ya kuma gode wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar nauyin taron na tsawon kwanaki uku a Kano.
A ƙarshe, shugaban CORECOEN na ƙasa kuma Magatakardar Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a ta Ringim da ke Jihar Jigawa, tare da Malam Nasiru Bala, Magatakardar Kwalejin Ilimi ta Gumel kuma shugaban ƙaramin kwamitin taron, sun bayyana cewa sabon tsarin babbar nasara ce, duk da ƙalubalen rashin wadatattun gine-gine da malamai a wasu kwalejojin ilimi na Nijeriya.
Sun ce duk da cewa Gwamnatin Tarayya na ƙoƙari, akwai buƙatar a taimaka wa kwalejojin cikin gaggawa domin samun nasarar shirin sauya tsarin karatu daga NCE zuwa digiri a kwalejojin ilimi.
Taron ya samu halartar wakiliyar ƙaramar Ministar Ilimi ta Nijeriya, masana, rijistirori daga kwalejojin ilimi daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki, waɗanda suka gabatar da maƙaloli domin taimakawa wajen samun nasarar sabon tsarin a Nijeriya.
