Tsananta adawa ko biyayya ga gwamnati daga ɓangaren majalisa na lalata shugabanci nagari – Masana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masana kimiyyar siyasa sun gargaɗi ’yan siyasa cewa tsananin adawa da gwamnati ko kuma goyon bayanta ba tare da yin nazari da tantance ayyukanta ba, dukansu barazana ne ga ingantaccen shugabanci a tsarin dimokuraɗiyyar shugaban ƙasa.

Farfesa John Ayoade, Farfesa Emmanuel Ojo da Dakta Babatola Gboyega Akinsanmi ne suka yi wannan gargaɗi a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka sanya wa hannu ranar Lahadi, inda suka bayyana ra’ayoyinsu a cikin sabon littafinsu mai taken The Handbook of Legislative Oversight (Jagorar Ayyukan Sa-ido na Majalisa). Masana sun bayyana cewa a tsarin dimokuraɗiyyar shugaban ƙasa, ɓangarorin gwamnati guda uku ya kamata su kasance suna aiki tare domin cimma manufa guda ɗaya, wato samar da ingantattun ayyuka da za su amfani al’umma.

A cikin sanarwar, sun yi cikakken bayani kan muhimmancin aikin sa-ido da majalisa ke yi wa hukumomin gwamnati a tsarin mulkin dimokuraɗiyya a faɗin duniya. Sun bayyana cewa wannan aiki wani muhimmin ɓangare ne na ingantaccen tsarin da aka tanada domin tabbatar da cewa kowace ɓangaren gwamnati na sa ido kan sauran ɓangarorin, tare da daidaita ayyukansu da kuma tabbatar da inganci.

Sun jaddada cewa sa-ido da majalisa ke yi wa ayyukan gwamnati shi ne ginshiƙi a tsarin dimokuraɗiyya, don haka wajibi ne ’yan majalisa su tabbatar da kare wannan aiki, ƙarfafa shi da kuma ci gaba da inganta shi. A cewarsu, wannan aiki yana daga cikin muhimman nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu, kuma yana cikin amana da alƙawarin da suka ɗauka na wakiltar al’umma.

Sun ƙara da cewa yin dokoki ba tare da sa-ido kan yadda ɓangaren zartarwa ke aiwatar da su da sauran ayyukansa ba, a zahiri yana rage wa majalisa muhimmancinta, domin hakan na bai wa ɓangaren zartarwa cikakken ’yancin yin abin da ya ga dama ba tare da kulawa ba. A cewarsu, sa-ido wani tsari ne na sanya ido da daƙile kura-kurai, wanda ke jagorantar yadda hukumomin gwamnati ke gudanar da ayyukansu.

Masanan sun ce idan aka bar irin wannan yanayi ya wanzu, hakan zai raunana manufar da ke tattare da raba ikon gwamnati zuwa ɓangarori daban-daban, wadda aka tsara domin hana wani ɓangare yin amfani da iko fiye da kima. Hakan ba wai kawai zai mayar da majalisa tamkar wata hukuma marar amfani ba ne, har ma zai haifar da gibi a aikin wakilcin al’ummar da aka zaɓi ’yan majalisar domin su wakilta. Sun ce: “Majalisar da ta miƙa wuya, da gangan ko ba da gangan ba, ta bar yin amfani da haƙƙinta da ikonta na sa-ido, to ta yi watsi da nauyin da aka ɗora mata da kuma yarjejeniyar amana da ta ƙulla da al’umma. Irin wannan bijirewa daga aikinta, ko da da wani dalili aka yi ta, cin amanar al’umma ne da kuma haƙƙin da aka ba ta.”

Bayan nazarin hujjoji da bayanai daga ƙasashen Afirka masu tsarin dimokuraɗiyya, masana sun kuma bayyana cewa kyakkyawar alaƙa tsakanin majalisa da ɓangaren zartarwa na buƙatar daidaito tsakanin haɗin kai da adawa. A zahiri, suna ganin ya kamata dangantakar ta kasance irin ta haɗin kai mai ɗauke da saɓani a wasu lokuta, domin tabbatar da cewa kowane ɓangare na gudanar da aikinsa yadda ya kamata. Sun bayyana cewa idan aka karkata wannan daidaito zuwa ga adawa mai tsanani, kamar yadda aka gani a lokacin da Ghali Na’Abba ke jagorantar Majalisar Wakilai, yayin da Olusegun Obasanjo ke shugabancin Nijeriya, aikin sa-ido na majalisa kan koma rigingimu da gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

A ɗaya ɓangaren kuma, idan dangantakar ta yi tsananin daɗi da kusanci, majalisa kan rasa matsayinta na mai sa-ido, ta koma wata hukuma da ke amincewa da duk abin da gwamnati ta gabatar mata ba tare da bincike ko tambaya ba. Sun ce duk waɗannan matsaloli suna kawo cikas ga shugabanci nagari, kuma daidaiton alaƙar ya fi fuskantar barazana a lokacin da jam’iyyun siyasa daban-daban ke da iko da majalisa da kuma ɓangaren zartarwa.

Sai dai sun jaddada cewa hakan ba yana nufin cewa ba za a iya samun barazanar ga wannan daidaito ba ne idan jam’iyya guda ce ke da iko da ɓangarorin biyu. A cewarsu, ɓangarorin gwamnati guda uku ya kamata su kasance masu aiki tare domin yi wa al’umma hidima yadda ya kamata. Sai dai kuma, suna iya samun bambancin fahimta kan abin da ya fi dacewa da al’umma, da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin cimma wannan manufa.

Sun jaddada cewa, “Abu mafi muhimmanci shi ne fahimtar cewa tsananin adawa da gwamnati, kamar yadda goyon bayanta ba tare da yin nazari da tantance ayyukanta ba, dukansu maƙiyan shugabanci nagari ne.”

By ukarofi